Gidan sayar da abincin N30 da ya yi suna a watannin baya a Kano ya kulle sakamakon tsadar kayan abinci da na masurufi.
Idan za a iya tunawa, gidan abincin ya yi suna ne a bara bayan Ministan Harkokin Noma, Sabo Nanono ya ce mutum zai iya samun
abincin N30 da zai kosar da shi a Kano.
Jin hakan ya sanya wani da ake kira Haruna Injiniya bude gidan abincin
da ake sayar da kwano shinkafa da wake da kuma garin rogo a kan N30,
ya kuma yi tashe.
Wakilin Aminiya ya waiwayi gidan abincin, da ke Layin Kuka, unguwar Sani Mai-Nagge, cikin birnin Kano, amma ya tarar da shi a kulle.
A tattaunawarsu da Haruna, wanda har ya koma sana’arsa ta gyaran kayan laturoni, ya shaida wa Aminiya cewa hauhawar farshin kayan abinci ta sanya shi daina sana’ar abincin.
“Kasuwa ba za ta yiwu ba da tsananin hauhawar farashin kayan abincin
da ake fama da ita.
“Abubuwa sun sauya, a yanzu kwanon gari da muke saye N200 ya koma
N600, kwanon shinkafa ya tashi daga N400 zuwa N1,300, haka na kayan miya.
“Na kafa gidan abincin ne da niyyar taimaka wa masu karamin karfi amma hakan ba zai yiwu ba”, inji Haruna.
Ya kara da cewa, “Ina kira ga Shugaban Kasa ya dubi talaka da fakirai
da ke cin abinci da kyar a yanzu da idon basira”.
Haruna ya kuma ce matsalar annobar COVID-19 da dokar kulle na daga cikin abubuwan da suka kawo tabarbarewar abubuwa.
“Mun yi kokarin ci gaba da sana’ar na watanni biyar a N30, amma da aka kulle gari, sai muka kasa tafiyar da gidan abincin muka kulle shi.
“Masu siya sun ji matukar haushin kulle sana’ar amma na ba su hakuri”, a cewarsa.
Haruna ya ce, akwai mata masu dafa abinci goma sha daya da biyar masu raba abinci, amma duk ya sallame su daga aiki.
“Abin alfahari ne. Mun nuna wa mutane cewar da naira 3000, mutane dari na iya cin abinci.
“Mun fara asana’ar da dafa buhu daya na shinkafa da gari, amma kafin kulle gari da aka yi sai da muka rika dafa buhu biyu”, inji Haruna.
Ya ce matarsa ce ta kirkiri bude gidan abincin cikin wasa, lokacin da suke tattauna maganar da ministan ya yi.
“Ta nace cewar maganar ministan tana kan hanya amma ban yarda sai da muka jaraba.
“Mun fara kasuwancin da kudi N450; Muka siyo garin N25 da man gyadan N50 da kulin N100 da cittar N20 da magin N20 da gishirin N20 — jumlar kudin ta kama N450.
“Bayan mun sayar muka samu N700, watau mun samu
ribar N250 ke nan, daga baya ne muka kirkiri wake da shinkafa”, inji
Haruna.