Tsadar kudin rajista ya kusa korar rabin daliban jami’a —ASUU

Shugaban Kungiyar ASUU ya ce karatu zai gagari rabin daliban jami’a, muddin gwamnati ba ta hana jami’o’in karin kudin rajistar barkatai ba

Tsadar kudin rajista ya kusa korar rabin daliban jami’a —ASUU

Jami’an ASUU

Shugaban Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU), Farfesa Emmanuel Asodeke, ya ce akwai yiwuwar ilimi zai gagari kimanin rabin daliban jami’a, nan da shekara biyu masu zuwa, muddin gwamnatin tarayya ba ta hana jami’o’in karin kudin rajistar da suke yi barkatai ba.

Farfesa Osodeke, wanda ya koka a bisa karin kudi barkatai da jami’o’in ke yi, ya shawarci gwamnati da ta bullo da tsare-tsare da za su ba wa dalibai damar karo ilimi cikin sauki.

A cewarsa, “yanzu jami’o’i sun koma karin kudi yadda suka ga dama. Shin ina hakan ya dace da halin da ake cikin na N30,000 a matsayin mafi karancin albashi? Ga tsadar kudin mota da na sufuri?”

Da yake magana a hirar da gidan talabijin na Channels ya yi da shi, Farfesa Osodeke ya ce, “Idan ba gwamnati ba ta hana karin kudin makarantar da ake yi a kasar nan ba, to kafin shekara biyu masu zuwa kashi 40 zuwa 50 na dalibai sai dai dau hakura da zuwa makaranta.”

Farfesa Osodeke ya yi gargadi cewa rashin zuwan matasa makaranarta babbar matsala ce ga ksar, “domin za su zama ’yan koron wadanda ke neman hana kasa a zauna lafiya.

“Abin da muke so shi ne a inganta fannin ilimi kamar na shekarun 60s da 70s; lokacin da nake makaranta gwamnati har alawus take ba ni na kasancewata dalibi, kuma a lokacin dan talaka na iya samun ilimi.

Amma “yanzu ta ina mai karbar albashin N50,000 zai iya biya wa dansa kudin makaranya N300,000?”

Shugaban na ASUU ya roki gwamnati ta kara kason bangaren ilimi zuwa kashi 15 cikin 100 a kasafin kudinta, domin kashi 3.8 da ta ware a kasafin 2023 babu abin da zai yi.

A cewarsa, idan aka kara kason da ake ba wa bangaren,  hakan zai rage wa iyayen dalibai tsadar kudin makarantar da za su biya.

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano