Tsadar Raguna Ta Sa Masu Shirin Layya Cikin Damuwa

Masu sayar da ragunan Layya a kudancin Najeriya suna kokawa da rashin masu saya a sakamakon matsin tattalin arziki da karancin kudi da jama’a a kasar nan ke fama da su. Aminiya ta ziyarci kasuwar da ake sayar da raguna a yankin Karamar Hukumar Kalaba ta Arewa a Jihar Kuros Riba. Alhaji Mukhtar Ahmad Sheka, […]

Tsadar Raguna Ta Sa Masu Shirin Layya Cikin Damuwa

Masu sayar da ragunan Layya a kudancin Najeriya suna kokawa da rashin masu saya a sakamakon matsin tattalin arziki da karancin kudi da jama’a a kasar nan ke fama da su.

Aminiya ta ziyarci kasuwar da ake sayar da raguna a yankin Karamar Hukumar Kalaba ta Arewa a Jihar Kuros Riba.

Alhaji Mukhtar Ahmad Sheka, shugaban kasuwar, ya yi karin haske dangane da yadda kasuwar ke ci da kuma matsalolin da ake ciki.

Ya ce, “Abin ya kasance ba kamar bara ba saboda a shekarar da ta gabatar ragon da ake sayarwa a Naira dubu 250, bana ana sayar da shi dubu 450, wannan kuma wani yanayi ne da ubangiji Ya kawo mu.

“Kuma a tawa fahimta akwai taka rawar shugabanni komai ya yi tsadar tun daga dabbobin da ma kowane abu na Najeriya ya zama abin da ya zama kai ya ninka kudinsa.”

A fahimtar dan kasuwar, babu abin da yake ganin ya kawo tsadar ta dabbobi da na sauran kayan “illa gwamnati don akwai hanyoyin da nake gani kamar yadda moma da taki sukayi tsada, saboda a noma ne ake samun abincin mutanen daban.

“Farashin dabbobi  ya ninka tunda ta hanyar noman ne ake samun sbinci ake samu a fitar da abincin da za a ba dabbobin, to ashe idan haka ne yadda abinci ya ninninka dole itama dabba ta ninka,” in ji shi

Kazalila dan kasuwar nada ra’ayi cewa cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi shi ma ya kara ingiza matsalar da kowa yake ji a jikinsa.

“Ba mutum ne kaɗai yanzu yake ji a jikinsa ba, hatta dabbobi ma da ake ciyarwa yanzu aua ji a jikinsu yasan an samun canjin al’amura na rayuwa don haka ba sai lallai dabbobin ni’ima ba da muke amfani da su hatta bera ma wannan ya san haka,” in ji dan kasuwar
Mafita inji shi ita ce “Mu koma ga Allah, karshe ya ce ya sayar da rago mafi sauki akan kudi Naira dubu 450 a kasuwar.