Tsadar Rayuwa: Dole ce ta sa muka ɗauki matakai masu tsauri — Tinubu

Tinubu ya ce da zarar matakan sun fara aiki, ‘yan Najeriya za su fara sharbar romon dimokuraɗiyya.

Tsadar Rayuwa: Dole ce ta sa muka ɗauki matakai masu tsauri — Tinubu

Shugaban Kasar Nejeriya, BolaAhmed Tinubu.

Shugaba Bola Tinubu, ya yi martani game da tsadar farashin man fetur, inda ya bayyana cewar, ya zama wajibi a ɗauki tsauraran matakai domin samar wa Najeriya ci gaba.

Tinubu, ya bayyana haka ne birnin  Beijing na China jim kaɗan bayan ganawa da wasu ’yan Najeriya.

Ya ce, ya zama tilas a ɗauki matakin ƙara farashin litar man domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan.

A yayin ganawar, Tinubu, ya ce “Najeriya na kan samar da sauye-sauye, kuma muna ɗaukar tsauraran matakai da ba a taɓa ganin irinsu ba. Misali, za ku riƙa samun labari daga gida game da farashin man fetur.”

Har wa yau, ya ce matuƙar aka daure waɗannan matakai suka fara aiki, za a ga alfanunsu da kuma irin hangen da yake yi wa Najeriya wajen kamo China a ci gaba.

Ya bayar da misali da kayayyakin more rayuwa da China ke da su da suka haɗa da kyawawan hanyoyi da wadatacciyar wutar lantarki mara yankewa da tsaftataccen ruwan sha da makarantu masu inganci.

Tinubu, ya bayyana cewa, burinsu a matsayinsu na shugabannin Najeriya, shi ne su gadar wa yaran da ke tasowa yanayi mai kyau.

Wannan na zuwa ne bayan Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL), ya ƙara farashin litar man fetur daga Naira 568 zuwa Naira 855.

’Yan kasuwa kuwa, na sayar da litar tsakanin Naira 930 zuwa 1,200.

Tun lokacin da shugaba Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur a watan Mayun 2023, al’amura suka fara ta’azzara a Najeriya.

Lamarin da ya haddasa tashin farashin kayayyaki tare da durƙushewar ƙananan sana’o’i.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025