Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya za ta fara rabon hatsi
Ministan ya ce za a fara rabon hatsin ne don rage wahalar da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
Gwamnatin Tarayya za ta fara rabon hatsi a fadin kasar nan, domin rage wahalar tsadar rayuwa da ake fuskanta a Najeriya.
Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari ne, ya wallafa hakan a shafinsa na X (Twitter), a ranar Litinin.
- Kar Ku Rika Biyan Kudin Gyaran Transfoma —Kamfanin JED
- Mutum 12 sun rasu, 28 sun ji rauni a hatsarin mota a hanyar Kano
“A wannan yanayi da ake ciki, ina mika jaje na ga wadanda wahalar da ake ciki ta shafa a kasar nan. Na fahimci girman al’amarin, musamman ga wadanda ba su da abin yi.
“Ina so na tabbatar muku cewa sadaukarwar da muka yi don jin dadinku ba za ta tashi a banza ba. Za mu fara rabon tan 42,000 na hatsi, kamar yadda mai girma shugaban kasa, ya amince a fadin jihohi 36 na tarayyar Najeriya don rage radadin halin da ake ciki.
“Muna aiki kafada da kafada da hukumar NEMA da kuma DSS domin ganin cewa hatsin ya kai ga wadanda suka dace su rabauta. Bugu da kari kuma, za a sake fitar da tan 58,500 na shinkafa zuwa kasuwa domin daidaita farashin kayan abinci.”
Ministan, ya roki ’yan Najeriya da su mara wa gwamnatin shugaba Tinubu baya a yunkurinta na magance kalubalen da kasar ke fuskanta.
“Na san irin halin da al’ummar Najeriya ke ciki, kuma na san wannan shugaban zai jagorance mu a halin da muke ciki. Mu tashi tsaye domin mara wa shugaban kasa baya a kokarinsa na ganin Najeriya ta inganta,” in ji Kyari.
“Gwamnatinmu a karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta himmatu wajen magance wadannan kalubale da kuma yin aiki don samar da makoma mai tsaro da wadata ga kowa a kasar nan.”