Tsadar rayuwa: Kotu ta ba da belin masu zanga-zanga a kan N10m kowannensu
Kotu ta tsare samarin da suka yi zanga-zangar tsadar rayuwa a Gidan Yarin Kuje, bayan ba da belin kowannensu a kan Naira miliyan 10.
Babbar Kotun Tarayya ta ba da belin samarin da aka kama a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa a kan Naira miliyan 10 kowannensu.
A ranar Juma’a Mai Shari’a Obiora Egwuatu na kotun da ke zamanta a Abuja ya kuma ba da umarnin tsare matasan su 76 ’yan kasa da shekaru 18, a gidan yarin Kuje har sai an cika sharuɗɗan belin.
Kotun ta sharɗanta cewa wajibi ne wanda duk mai tsaya wa kowannensu, ya kasance babban ma’aikacin Gwamnatin Tarayya da ya mallaki lasisin tuƙi da kuma lambar shaidan ɗan ƙasa.
Wajibi ne kuma waɗanda ake zargin su gabatar da takardar shaida daga iyayensu ’yan uwa.
Daga nan ya bayar da umarnin tsare su a gidan kula da kangararrun yara da ke Gidan Yarin Kuje, zuwa lokacin da za a cika sharuɗɗan belin.
Ya kuma sanya 24 ga watan Janairu 2025 a matsayin ranar ci gaba da sauraron shari’ar.
Gwmanatin Tarayya ce ta gurfanar da waɗanda suka shiga zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a watan Agusta, 2024 a Jihohin Kano da Kaduna da sauransu, inda take tuhumar suna laifuka 10.