Tsadar rayuwa: Malaman jami’a sun koma kwana a ofis
Malaman jami’o’in gwamnati a Nijeriya sun koma kwana a ofisoshinsu saboda tsadar mai da tashin gwauron zabon kayan masarufi a kasar
Malaman jami’a a Nijeriya sun koma kwana a ofisoshinsu sakamakon tsadar mai da sauran matsalolin tattalin arziki da suka haifar da tashin gwauron zabon kayan masarufi.
Tsadar man fetur da kayan masarufi a qasar ta sa wasu daga cikin malaman daina hawa motocinssu sun koma hawa na haya zuwa wurin aiki, tare da daukar wasu matakai domin rage kashe kudi.
Wasu malaman kuma sun hakura da karatun digiri na uku da suke yi, saboda rashin kudi a wannan yanayi da tsadar rayuwa da ta yi wa ‘yan kasar katutu.
Wani bincike da jaridar Vanguard ta gudanar ya gano yadda wasu lakcarori a Jami’ar Jos suka koma takawa a kafa ko hawa motocin haya domin zuwa aiki.
- Naja’atu da Bafarawa sun kafa sabuwar tafiyar matasan Arewa
- Fintiri ya rage ikon Lamiɗon Adamawa zuwa ƙananan hukumomi 3
A Jami’ar Jihar Legas (LASU) wasu malamai sun koma kwana a ofisoshinsu da ke harabar jami’ar domin rage kudin da suke kashewa kullum wajen zuwa koyarwa a duk mako.
Tarewar tasu a ofisoshinsu ta saba wa tsarin jami’ar na rashin kwana a harabarta, lamarin da hukumar jami’ar gargadi ga masu yin hakan, saboda abin da ta kira dalilan tsaro.
Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta bayyana damuwa kan mummunan yanayin da lakacarori ke shiga, tana mai kira ga gwamnati da ta shawo kan matsalar rashin isassun gidaje da rashin isasshen albashi, duba da yanayin tsadar rayuwa a Nijeriya.
Ita ma Kungiyar Daliban Nijeriya (NANS) ta bayyana cewa halin da malaman ke shiga kai tsaye yake shafar karatun dalibai. Don haka suka roki gwamnati da ta hanzarta daukar matakin magance matsalolin da ke ci wa lakcarorin tuwo a kwarya.
Gwamnatin Tarayya, a nata bangaren ta cewa tana sane da halin da malaman suke ciki, kuma a halin yanzu ta ba da fifiko ga jin dadinsu.
Amma wasu da dama na ganin akwai bukatar gwamnatin ta kara azama wajen magancee matsalar.