Tsadar rayuwa: Matasan Nijeriya suna tururuwar tafiya ƙasashen waje
Ban bai wa kowa kuɗi ba, ta cikin kasar Nijar na bi na ƙetare zuwa kasar Aljeria tare da taimakon dan uwana.
Yanayin rayuwar da ake fama da shi a Nijeriya ya tsunduma miliyoyin ’yan kasar cikin talauci da rashin aikin yi.
Abin ya fi kamari a Arewacin kasar sakamakon fama da suke da rashin tsaro da karancin ababan more rayuwa da kuma rashin ci-gaban al’ummar.
- Shin taƙaddamar Murja da Hisbah na da nasaba da murabus ɗin Sheikh Daurawa?
- CBN ya soke lasisin ’yan canji 4,173 a faɗin Nijeriya
A wannan rahoton, Aminiya ta bankado wani sabon salo da yake nuna yadda matasan Arewacin kasar ke barin kasarsu ta haihuwa domin neman mafaka da ingantacciyar rayuwa a yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.
Bayan kwashe kusan shekara biyar da kammala digiri ba tare da samun aikin ba, hakan ya sa Hassan Dantsoho ya fara shirye-shiryen barin kasar domin zuwa kasar Kuwait, daya daga cikin kasashen duniya masu arzikin man fetur, domin neman ingantacciyar rayuwa.
Matashin mai shekara 30, ya kammala shirye-shiryen hijirarsa zuwa kasar Kuwait a cikin watan Fabarairu, har ma ya fara bankwana da ’yan uwansa da ke Kano, tare da kiyasta samun arzikin akalla Naira miliyan 40 a zaman da zai yi na shekara biyu kacal.
“Idan abubuwa suka tafi daidai yadda nake so a kasar Kuwait, burina shi ne ni ma na zama wakilin da zai riƙa yi wa ma’aikatan lafiya da masu kananan sana’o’i ’yan Nijeriya masu burin zuwa kasashen waje hanyar ficewarsu,” cewar matashin a watan Disambar da ta gabata yayin zantawarsa da wakilinmu.
Matashin ya kara cewa: “Misali idan ka dauki sana’ar gyaran famfo, dan Nijeriya a Kuwait zai iya samun albashin akalla Naira dubu dari shida duk wata saboda su Larabawan ba sa yin irin wadannan kananan ayyukan.”
Sakamakon fama da rashin aikin yi, Dantsoho na daya ne daga cikin dubban ’yan Nijeriya daga Arewacin kasar wadanda tsananin rayuwa ke sawa suna burin barin kasar don neman mafita a kasashen ketare, irin su Kuwait da Katar da Aljeriya da sauran kasashe da ke yankin Gabas ta tsakiya da Arewacin Afirka.
Kungiyar Adana Bayanan Hijira ta Duniya wato (IOM) ta bayyana yadda dandazon ’yan Njieriya kimanin mutum 241, 121 suka yi bar kasar zuwa kasashen ketare a 2022.
Bayanan da aka tattaro daga kundin gwajin lafiyar matafiyan ya nuna cewa, kimanin mutum 196, 695 daga Nijeriya sun bar kasar zuwa kasar Birtaniya.
Kimanin mutum 40, 706 sun je kasar Kanada da kuma mutum 2, 428 zuwa kasar Amurka.
Hakazalika, bayanan sun nuna kimanin 3,280 sun yi hijira zuwa kasar Austiriya sai kuma mutum 12 zuwa wasu kasashen.
Wata kididdiga da aka fitar daga kundin gwajin lafiyar matafiyan ta nuna cewa, adadin ’yan Nijeriyar da suka bar kasar a 2022 sun ninka adadin wadanda suka fice daga kasar a 2021 da wajen karin kaso 127.5, musamman zuwa kasashen Birtaniya da Amurka da Kanada da Austiriya.
Wannan sabon salon barin kasar ya yi daidai da wani bincike da kungiyar da ke kula da al’amuran da suka shafi hijira ta yi a 2023, wanda ya gano cewa, adadin ’yan Nijeriya da ke zaune a kasashen ketare ya nunka sosai daga 1990 zuwa 2020.
Adadin ya tashi sosai daga 447, 411 zuwa 1,670, 455 wanda kaso mafi rinjaye daga cikin ’yan Nijeriya mazauna kasashen ketaren sun fito ne daga yankunan Kudu maso Kudu da Arewa ta Tsakiya da kuma Kudu maso Yamma na Nijeriya.
Sai dai kuma wani binciken da Aminiya ta yi ya nuna abin takaici na yadda matasan Arewacin Nijeriya ke rigerigen barin kasar zuwa kasashen yankin Gabas ta tsakiya da kuma Arewacin Afirka.
Abin da ya sa muke barin kasar — Matasan Arewa
Daga can cikin Madigawa, wata unguwa mai cike da al’adun gargajiya da na zamani a birnin Kano, Hassan Abdulsalam mai shekara 27 ya samu damar ketarewa zuwa kasar Aljeriya domin sana’ar dinki.
Matashin ya ce, bayan shekara ɗaya da tafiyarsa, ya dawo gida da ɗimbin arzikin da ya siya masa fili har ya gina masa gida a garin Kano.
Sai dai kuma ya ce, yanzu yana hankoron tafiya kasar Katar ne domin neman wani arzikin.
“Ban bai wa kowa kuɗi ba, ta cikin kasar Nijar na bi na ƙetare zuwa kasar Aljeria tare da taimakon dan uwana, wanda yake a can kasar, har Allah Ya kaddara ga shi na je, na dawo, na samu arziki sosai,” inji Hassan yayin da yake taka keken dinkinsa.
Hassan ya kuma ƙara da cewa, duk da cewa Aljeriya ita ma na fama da rashin ingantaccen tsaro, amma sana’ar dinkin keke tana daga cikin sana’o’in da ake samun kudi sosai, musamman ga bakin da suka je Aljeria kuma suke da wata sana’ar hannu.
A wani labarin kuma, Hassan Dantsoho ya kammala dukkanin shirye-shiryensa domin yin hijira zuwa kasar Kuwait, inda yake da burin zama wakilin masu niyyar zuwa kasar.
Ya ce, yana nan ya kara kulla alaka da manyan kamfanoni da suke da bukatar ma’aikata ’yan Nijeriya, musamman ma’aikatan lafiya.
“Idan kana aikin likita a kasar Kuwait, akalla za ka samu albashi kimanin Naira miliyan shida duk wata. Ka ga da wannan kudin, ai mutum ba ya bukatar dawowa Nijeriya, sai dai ma ya gina asibitin kansa,” cewar Dantsoho.
Aliyu Ibrahim, shi ne mai kamfanin Alkiswa, wanda ke aikin sufuri da zirga-zirgar maniyyata Hajji da Umara a Kano, ya ce tabbas wannan mafarkin na matasan Arewacin Nijeriya da ke kokarin ficewa daga kasar zuwa yankin Gabas ta Tsakiya domin neman aikin yi gaskiya ce, domin kuwa kamfaninsa yana samun tuntuba da yawa daga wajen irin waɗannan matasan a kowace rana.
“Mutane da dama suna zuwa wajenmu saboda suna son su bar kasar. Amma babbar matsalar ita ce, mafi yawancinsu ba su da kuɗin kuma ba su da takamaiman dalilin da ya sa suke son tafiyar.
“Kawai za ka ji sun ce su dai sun gaji da wahalar rayuwar da ake a Nijeriya, suna son su tafi neman kudi a wata kasar.”
Ya kara bayanin cewa, mafi yawan kasashen da ake zuwa sun hada da Dubai da Katar da Jodan da Saudi Arabiya.
Aminiya ta gano cewa, akalla matasan Arewa na biyan kudi tsakanin Naira 700,000 zuwa miliyan uku ga wakilai irin su Ibrahim, domin cim ma burinsu na barin kasar zuwa kasar waje.
Haka kuma, Aminiya ta gano cewa, kudin da ake biya ya bambanta kuma ya danganta da kasar da mutum yake sona zuwa da irin bizar da yake so, har ma da adadin tsahon lokacin da zai yi a kasar da kuma irin aikin da ya samu da albashin da zai rika dauka.
Sai dai Ibrahim mai kamfanin Alkiswa da ke hada-hadar maniyyata Hajji da Umara ya yi karin hasken cewa, mafi karancin abin da suke karba domin samar da takardun tafiyar ya kai akalla miliyan daya da dubu dari takwas.
Amma duk da haka, ya ce sai sun nemi tikitin jirgi sun saya.
“Mafi yawancin wadanda suka tafi Dubai suna ayyuka a kamfonin tura kaya da na alewa.
“Wadanda kuma suka tafi kasar Jodan suna aikin kamfanin takalmi. Wadanda suke Saudi Arabiya kuma suna aiki a kamfanin wankin mota da gidajen abinci.
“A kasar Katar kuma, yawancinsu suna aikin ne a wajen aski da gyara gashi,” Ya kara da cewa: “Muna da mutane da dama a kasar Jodan, waɗanda muke da dadaddiyar alaka, kuma muke taimaka masu ta hanyar nemo ’yan Nijeriya wadanda suke da sha’awar zuwa can domin yin aiki a kamfanin takalmi.
’Yan Nijeriya da suke barin kasar suna cikin halin ha’ula’i, cewar mazaunin Katar
Daf da Gasar Kofin Duniya a 2022, Gwamnatin Katar ta yi kiyasin cewa, akalla gasar za ta samar da ayyukan yi a bangaren gine-gine sama da miliyan ɗaya da rabi.
Shugaban ofishin jakadancin kasar Katar a Nijeriya, Ahmad Al-Horr a watan Agusta na 2022 ya nemi kulla yarjejeniya tsakanin Nijeriya da Katar domin samar wa ’yan Nijeriya guraben aiki.
A cewarsa, “Katar na buƙatar ma’aikata ’yan Nijeriya a bangaren ayyukan karfi.”
Duk da cewa kammala wasannin Gasar Kofin Duniyar ya rage buƙatar ma’aikata ayyukan karfi a kasar Katar, har yanzu matasan Arewacin Nijeriya ba su daina marmarin zuwa kasar ba.
Abdulwahid Ibrahim dan asalin Jihar Kano, wanda ya kware a sana’ar dinkin hannu irin na rigunan gargajiya amma yanzu haka zuciyarsa ta karkata zuwa tafiya kasar Katar domin neman arziki.
Matashin mai shekara 29, ya ce, ya ba da kuɗi Naira dubu dari shida domin a samo misa tikiti da biza domin tafiya kasar, inda ya ce an yi masa alkawarin aiki a kamfanin lemo, wanda yake sa rai zai samu kudin da zai biya bashin da ake bin sa tare da taimaka wa ’yan uwansa.
“Tun daga nan za ku iya yin yarjejeniyar biyan kuɗin gaba ɗaya ko kuma ka biya wani bangare daga kudin, tare da amincewar idan suka kai ka kasar, ka fara aiki, za su rika cire wani kaso daga cikin albashin har zuwa lokacin da za ka gama biyan kudin.
“Sai dai ni ma na bayar da wani bangare na kudin, kuma sun amince idan na fara aiki a can zan karasa biyan ragowar.”
Abdulwahid ya kara da cewa, “yanzu haka abokaina da dama na aiki a kasar, shi ya sa nake burin zuwa can. Yanzu kawai biza ta nake jira.”
Rayuwa a Katar, ba kamar yadda Ibrahim da sauran matasan Arewa ke tunani ba ne, a cewar Yusuf Isah (ba asalin sunansa ba ne).
Ya ce, ‘yan Nijeriya da dama a takure suke. “Wallahi, na san mutane da dama da ba su da aiki da wajen fakewa.
“A cikin kwana uku kacal, sama da mutum 70 har da ’yan uwana huɗu suka koma Nijeriya daga Katar dalilin rashin abin yi.
“Kawai sun nemi alfarmar Gwamnatin Katar ne su koma da su gida kyauta,” in ji shi.
Isah, wanda ke zaune a Katar sama da shekara daya ya ce, “a nan akwai ma’aikatar gwamnatin da ke kula da irin wannan lamari ba tare da karbar ko sisi ba.
Kawai abin da ake buƙata shi ne mai buƙatar komawa kasarsa, zai cike wasu takardu da yarjejeniyar cewa ba zai dawo ba har sai bayan shekara biyar.”
Ya shaida wa Aminiya cewa, masu zuwa kasar sun fi ayyukan da ke kasar yawa.
Ya kara da cewa, duk da rashin aikin, ’yan Katar sun fi yarda da ’yan ƙasashen Uganda da Kenya da Sudan da Bangladash da kuma Philippines fiye da ’yan Nijeriya.
Ya kara da cewa, sabanin yadda ake ba wa ’yan kasar Uganda dama su fara aiki kamin a ba su takardar shaidar lafiya, ’yan Nijeriya ba su da wannan damar domin sai an tantance su kafin su fara aiki a Katar.
Ba mu da matsala da masu barin kasar — Hukumar Hijira ta Nijeriya
Hukumar Hijira ta Nijeriya (NIS) ta ce, in dai har mutane sun bi ta hanyoyin da suka kamata wajen barin kasar, ba su da matsala da hakan. “Yin hijira dole ne a rayuwa.
“Mutane sun saba yin hijira don cika wasu muradansu na rayuwa, wanda zai iya zama domin neman arziki ko neman tsaro ko canjin yanayi ko neman ilimi.
“Ai ba laifi ba ne in mutane suka bar kasarsu zuwa wata kasar,” in ji kakakin hukumar, Adedotun Aridegbe.
Yayin da yake mayar da martani ta manhajar WhastApp, Aridegbe ya yi kira ga masu barin kasar su tabbatar suna da cikakkun takardun kasashen da suke da niyyar zuwa, domin hukumar tasu ba ta yarda da yin tafiya ba tare da cikakkun takardu ba ko bi ta hanyoyin da ba su dace ba.