Tsadar rayuwa: Mun kosa jihohi su raba mana tallafin —Talakawa

‘Rayuwarmu fa tana cikin kunci’ ‘Lokacin kamfe ne kawai aka san inda muke’

Tsadar rayuwa: Mun kosa jihohi su raba mana tallafin —Talakawa

Yayin rabon tallafi

A farkon watan Agusta ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta bayar da Naira biliyan biyar ga kowace jiha daga jihohi 36 da Abuja, domin su rage wa mutanensu radadin janye tallafin man fetur.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ne ya bayyana haka a Fadar Shugaban Kasa bayan kammala taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC), wadda Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya jagoranta.

Gwamnatin Tarayya ta ce ta yi haka ne domin rage radadin da ake ciki bayan cire tallafin man fetur, wanda ya jawo hauhawar farashin kayayyaki da tsadar sufuri da sauran harkokin rayuwa.

Haka kuma a wata sanarwa ta daban a lokacin, Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume ya ce an ba kowace jiha tirela 100 na taki da tirela 100 na hatsi domin rage radadin.

Sai dai tun a lokacin ne Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta fito ta bayyana rashin amincewarta da shirin, inda ta ce ba ta amince a ba gwamnoni kudaden ba.

Sakataren Kungiyar NLC, Mista Chris Onyeka ya bayyana a lokacin cewa ta ina gwamnoni za su raba kudaden tallafin, alhali wasunsu sun kasa biyan mafi karancin albashi.

Bayanai sun nuna cewa gwamnonin jihohi su suka fi matsawa a cire tallafin mai domin su samu kudin gudanar da ayyuka da sauke nauyin da ke kansu.

Sai dai kuma duk da makudan kudin kason tarayya da suka samu a wata biyu na wannan gwamnati sun gaza tsara wani shiri na tallafa wa jama’ar jihohinsu.

Kuma ana cikin haka ne suka matsa wa Gwamnatin Tarayya kan sai ta mika musu kudin tallafin da ta ware don su raba da kansu.

A yayin da aka mika wani kaso na kudin tallafin kuma mutane suke cikin mugun kuncin rayuwa sai gwamnonin jihohin suka kwanta a kan kudin ba tare da sun raba ba.

Kuma sai suka fara karkatar da kudin wajen yin wasu abubuwa da suka hada da cewa sun sayo ko za su sayo motoci da sunan tallafa wa sufuri.

Wannan ya nuna sun kimshe nasu kason ke nan ba su shirya komai don kyautata wa talakawan nasu ba.

Aminiya ta gano cewa a Jihar Borno ce kawai aka fara rabon tallafin kayan abincin ba tare da jiran tallafin Gwamnatin Tarayya ba, sai kuma Jihar Katsina da wasu da suka fara.

Amma wasu jihohin cewa suka yi sun sayo motocin sufuri, wasu kayayyakin abinci ko suna yunkurin sayowa da sauran shiryeshirye raba tallafin amma ba su fara ba. Wasu jihohin sun ce Naira biliyan biyu aka fara tura musu, ba biliyan biyar ba.

A Jihar Kaduna, tun bayan kaddamar da kwamitin rabon kayan tallafin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi a makon jiya, al’ummar jihar suke dakon ganin ranar da za a fara rabon.

A lakacin kaddamar da kwamitin wanda ke karkashin Mataimakiyar Gwamnan Jihar Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe Gwamna Uba Sani ya ce akwai kungiyoyin kwadago da na ’yan kasuwa da sauransu da aka sanya su a cikin kwamitin domin tabbatar da adalci.

Ya ce tuni ’yan kwamitin sun tattauna abin da za a yi da Naira biliyan biyu da jihar ta samu daga cikin Naira biliyan biyar da Gwamnatin Tarayya ta yi alkawari.

Daga cikin abubuwan da za a yi da kudin akwai raba kayan abinci ga talakawa da ’yan gudun hijira da sayo motocin sufuri don daukar mutane kyauta na tsawon wata shida kafin daga bisani a rage kudin sufurin domin saukaka wa mutane.

Akwai kuma shirin sayo taki domin raba wa manoma a kauyuka da kuma farfado da jirgin kasa domin saukaka wa mutane kudin sufuri daga Zariya zuwa Kaduna da kuma zuwa Kafanchan a Kudancin Jihar.

Gwamna Uba Sani ya ce kwamitin ya zauna da shugabannin kungiyoyi da malamai da sarakuna, inda suka yarda cewa za a yi amfani da kudin ne wajen sayen buhunan shinkafa 43,000 domin rabawa.

“Wanda za a tabbatar da cewa al’umma kusan miliyan daya da dubu 50 ne za su amfana da tallafin. Kuma wadanda za a fara da su su ne marasa karfi sosai.

“Kashi uku za a yi wajen ba da tallafin har da bangaren sufuri za a yi inda za a hada kai da kungiyar direbobi ta hanyar rage kudin sufuri ga jama’a su riga zuwa wuraren aikinsu cikin sauki,”inj i shi

Ya ce zai duba bangaren jiragen kasa domin farfado da jirgin da ke tasowa daga Zariya zuwa Kaduna da Kafancan domin al’umma su samu sauki.

Ya ce duk abin da za su yi sai sun sanar da al’umma kuma a cewarsa lokaci zuwa lokaci za su rika yi wa jama’a bayanin halin da ake ciki.

Mun ji shiru —Mazauna Jihar

Wasu daga cikin mazauna Jihar Kaduna sun ce har yanzu shiru suke ji dangane da batun rabon tallafin domin kuwa har yanzu ba a fara rabon ba.

Sarkin Makafin Tudun Wada, Malam Muhammad Bello Abubakar ya nemi a tuna da su wajen rabon ba a ba ’yan boko kawai ba.

Ya ce akwai bukatar a sanya sarakunan nakasassu irin su makafi da guragu don su karba a madadin mutanensu.

“Mu muka san inda talakawanmu suke kuma mu muka san masu bukata ta sosai da sosai. Muna farin ciki da wannan tallafi da za a bayar amma a yi mana adalci, musamman makafi,” in ji shi.

Ya bayyana cewa har yanzu ba a tuntube su ba dangane da rabon tallafin musamman su sarakunan makafi da na guragu da kutare.

Shi ma Malam Sadisu Usman wanda aka fi sani da (D.D Guy) a Kasuwar Barci ya ce jinkirin rabon kayan tallafin babu dadi domin sun matsu su ji an ce a je a karba.

Ya ce tallafin da so samu ne a maimakon a raba kayan abinci da motoci aka saya wadanda duk wani dan jiha zai amfana da su.

“Ya kamata a sayi wani abu da zai amfani kowa. Ma’ana kowane talaka zai amfana. Misali a sayi motoci a kai su inda mutane za su rika amfani da su domin samun saukin kudin mota,” in ji shi.

Game da ba gwamnonin damar rabon kudin tallafin ya ce hakan bai dace ba, kasancewar inda ba wadanda suke yi ba, ba kowa zai amfana ba.

“Misali idan aka ba Gwamnan wata jam’iyya ba lallai ba ne dan wata jam’iya ya samu saboda zai ce ai ba su zabe shi ba. Ka ga ke nan ba kowa zai samu ba.

“Idan shugabanin siyasa za a ba kudin su raba ai sai sun diba kafin su raba. Don haka ba kowa ba ne zai samu tallafin ba,”in ji shi.

Ya kara da cewa kamata ya yi su kansu gwamnonin su raba nasu tallafin ba tare da dogaro da na Gwamnatin Tarayya ba, domin su ma suna iya raba tallafi a matakin jiha.

Shi ma tsohon kansilan Unguwar Sarki Kaduna, Zubairu Shan’una ya ce batun ba da tallafin tun farko yaudara ce saboda an ce an bayar da Naira biliyan biyar ga kowace jiha ciki har da Kaduna gwamnonin sun fito sun ce biliyan biyu ta shigo asusun jiha.

“Idan ka dauki biliyan biyar ka sa ta cikin Jihar Kaduna tsakani da Allah me zai yi a irin halin da aka tsinci kai? A dauka ma za a ba mutum Naira dubu takwas a wata shida ai ba zai rage wa mutane radadin da suka tsinci kansu a ciki ba,” in ji shi.

Ya kara da cewa a baya an ba tsosaffin gwamnoni tallafin Kulob din Paris da sunan a taimaka wa talakawa wanda kuma ba su bayar ba. “Saboda haka ba su damar rabon kayan tallafin ba lallai ba ne jama’a su samu,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Gwamnan Jihar Borno daban yake da sauran gwamnoni domin shi mutum ne mai kishin al’ummarsa kuma ya fadi shi ba ma Naira biliyan biyar din yake jira ba har kara nasa tallafin ya yi domin raba wa talakawa.”

Mun shirya don fara rabon —Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce nan ba da jimawa ba za a fara rabon tallafin ga al’umma.

Kakakin Gwamnan Jihar Mohammad Lawal Shehu ne ya sanar da haka a lokacin da Aminiya ta tuntube shi.

Ya ce an kafa kwamiti a matakan kananan hukumomi bisa yardar babban kwamitin jihar. Su kuma masu rike da mukaman siyasa a kowacce karamar hukuma a matsayin masu lura.

Da aka tambaye shi ke nan har yanzu ba a sa ranar fara rabon ba sai ya ce “Nan ba da jimawa ba za a fara in sha Allah.”

A Jihar Kano, dubban mutane ne suka shiga halin talauci da damuwa tun bayan cire tallafin man fetur din da aka yi, wanda hakan ya sa suka fara kira a fara rabon kayan tallafin da aka sayo da kudin tallafin da Gwamnatin Tarayya ta turo.

Tun farko Gwamnan Jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi korafi game da daidaita jihar tasa da sauran jihohi da Gwamnatin Tarayya ta yi wajen rabon kudin inda ya ce kowa ya san dimbin jama’ar da Allah Ya albarkaci jihar da su don haka ya ce akwai bukatar duk lokacin da za a yi rabo irin wannan a rika yin la’akari da yawan al’ummar jihar.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto Gwamnatin Jihan Kano ba ta fara raba tallafin ga al’ummar jihar ba.

Sai dai Sakataren Watsa Labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatin za ta kaddamar da fara rabon, kuma ya ki cewa komai a kan yadda gwamnatin za ta tsara rabon tallafin.

Sai dai binciken Aminiya a jihar ya nuna cewa al’ummar jihar sun kosa tallafin ya zo gare su.

Malam Salisu Ado Sani ya bayyana cewa jinkiri da jan kafar da gwamnatin jihar ke yi wajen rabon tallafin da cewa ba ya da wani amfani illa kara cutar da al’ummar jihar.

“Gaskiya rashin bayar da tallafin nan da Gwmanatin Kano ta yi ba daidai ba ne domin a yanzu mutane suna kara shiga cikin tsananin rayuwa. A kullum gari ya waye sai ka ji mutane suna kukan talauci. A wasu wuraren ma mutane har mutuwa suke yi saboda yunwa,” in ji shi.

Ya yi kira ga gwamnatin ta gaggauta raba tallafin kafin mutane su kara shiga wani mugun hali.

Wata mai suna Malama Rabi Ali ta nuna damuwa game da rashin raba tallafin da Gwamnatin Kano ta yi, inda ta yi fata gwamnati za ta yi abin da ya dace idan aka tashi yin rabon.

“Tunda aka ce an kawo kudin tallafin muke ta saurare mu ji ranar da za a fara rabawa. Amma har yanzu shiru.

“Kuma ba a yi mana bayanin dalilin da ya hana a yi mana namu tsarin rabon ba. Ga shi kowa ya san halin da ake ciki, al’umma duk mun koma mabarata; mutum ya ci na yanzu, yana tunanin na in an jima.

“Muna kira ga gwamnati ta yi adalci wajen rabon kayan tallafin kada ya zama an kara wa masu karfi wani karfin da tallafin.

“Idan son samu ne gwamnati ta bayar da tallafin ta hannun masu unguwanni kasancewar su ne suke kusa da al’umma kuma su suka san kowane mutum da ke zaune a unguwarsu.

“Haka kuma su ne suka san yanayin wadatar mutanen da suke zaune a unguwanninsu da sauransu,” in ji ta.

Malam Ghali Sani ya ce “Tun da muka ji labarin gwamnati ta bayar da tallafin wallahi muke murna, sai dai kuma a yanzu murnarmu tana neman komawa ciki. Tunda ga shi har yanzu ba su fara raba kayan nan ba.”

Yawancin mutanen da Aminiya ta tattauna da su ba su soki damka rabon ga gwamnoni bisa la’akari da cewa tallafin zai fi saurin zuwa gare su ba idan daga jihohinsu za a raba.

“Mun ji dadin da aka ce a jihohi za a yi wa wannan rabon domin gwamnatin jiha ta fi kusa da al’mma a kan ta tarayya.

“Sai dai muna kira ga gwamnati ta yi wa Allah ta tsaya ta yi adalci wajen rabon yadda zai je ga talakawan da aka yi dominsu. Kuma muna rokon gwamnati da ta saya mana kayan abinci masu kyau ba rubabbu ko wadanda suka dade a ajiye ba, kamar yadda ya faru a wata jiha inda al’ummar jihar suke ta korafi a kan hatsin da aka ba su, suna cewa shara ce mai yawa a cikin hatsin.

“Haka kuma akwai bukatar gwamnati ta bayar da isasshen abinci ga jama’arta ba kwano daidai na hatsi ko taliya leda biyu kamar yadda ake cewa an raba a wasu jihohi ba,” in ji shi.

A ranar Litinin da ta gabata ce Sakataren Gwamnatin Jihar Adamawa Awwal Tukur ya gudanar da wani tsarin rabon kayan abinci domin rage tsadar rayuwa ga talakawan jihar.

Alhaji Tukur ya ce sun gudanar da tsarin ne domin ci gaba da ba da tallafi ga jama’a sannan ya ce kowane buhun shinkafa da ke da kilo 25 za a sayar da shi a Naira dubu goma.

Ya ce Naira biliyan biyu aka bai wa jihar domin ba da tallafin inda ya ce tsarin zai sanya a yi rabon cikin lumana.

Ya ce gwamnatin ta sayo motoci goma a kan Naira billiyan 1.6 domin samar da saukin sufuri sannan ya yi alkawarin gudanar da shirin bisa adalci.

Sai dai sabanin haka talakawa da dama sun koka da tsarin kamar yadda suka shaida wa Aminiya.

Muhammad Sani basarake ne mazaunin Jihar Adamawa ya ce an shiga kuncin rayuwa da ba a taba shiga ba a baya. “An shiga tsadar rayuwa wadda ko da kudin ba zai isa ka ci abin da kake so a gidanka ba. Shinkafa da masara duk sun yi tsada,” in ji shi.

Ya ce wata rana ya samu dan wani makwabtansu na shanya dusa saboda yana so ya tura Taraba a kai wa dabbobi domin a cewarsa an rasa dusa a Taraba saboda jama’a da dama ba su yin surfe haka suke nika abincin su ci.

“Gwamnatinmu ta Adamawa na kokari a wani wajen, sai dai sun dan jinkirta wajen ba da tallafi domin irin wannan jinkiri da yunwa da ta addabi jama’a ne suka sa marasa hakuri suka fasa rumbunan gwamnati domin samo abin da za su ci.

“Gwamnan Jihar Borno yana kokari shi ya sa ba su taba fasa rumbuna ba duk da da ’yan ISWAP da ’yan ta’adda amma ba su taba fasa rumbuna ba saboda gwamnansu da kansa yake raba kayan tallafi,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Gwamnatin Adamawa ta ce sai dai mu biya Naira dubu goma sannan a ba mu buhun shinkafa kilo 25. Mu da muke da karamin karfi an manta da mu ke nan? Ina za mu samu Naira dubu goma?”

Malam Garba Halilu wanda yake gadi ya ce ya shiga kuncin rayuwa na rashin abinci domin ganye yake zuwa ya samo a daji kamar zogale a kwada a ci, ga yara fiye da goma.

Ya ce a da yakan sayo shinkafa amma yanzu ba zai iya ba domin a cewarsa, gwangwanin shinkafa da ake saya Naira 80 a baya yanzu ya kai Naira 200.

Malam Halilu ya ce ba yai da halin da zai biya Naira dubu 10 domin sayen shinkafar tallafin, sai ya yi kira ga gwamnatin jihar ta yin ragwame ga mutane irinsu.

Wani matashi mai suna Malam Aliyu Isa ya ce kudin hawa Keke NAPEP ya yi tsada ba kamar da ba, inda mutum ke biyan Naira 50 yanzu sai ya biya Naira 150 ko 200.

Hafsatu Muhammed matar aure ta ce rayuwar ta yi wahala domin idan ba a samu abinci ba, sai dai a ga yara na kuka manya kuma fuska a daure.

Ta roki Gwamnatin Tarayya ta taimaka wajen mayar da tallafin kudin man fetur domin man fetur ya yi sauki kuma talaka ya samu abin da zai ci.

Ta kara da cewa idan abinci ya yi sauki talakawa za su kara fitowa zabe, amma idan suka wahala, ta ce ko zaben ba za su fito su yi ba.

Ta ce jarinta ya karye ga tsadar abinci sannan filin da suke zama ba nasu ba ne masu filin za su iya zuwa su tada su.

Malama Maimuna Abubakar ta ce rayuwa ta taba su, dama su take tabawa domin cire tallafin man fetur din nan su aka cire wa.

Ta ce ita da makwabtanta takawa suke yi duk inda za su je domin tsadar sufuri.

“Idan za a yi zabe ana sanin lungunan da muke amma idan tallafi ya zo kamar bata a hanya ake. Don Allah yadda ake shiga lunguna domin neman kuri’armu kada a manta da mu a wajen rabon tallafin,” in ji ta.

 

Daga Mohammed Ibrahim Yaba, Kaduna da Lubabatu I. Garba, Kano da Amina Abdullahi, Yola