Tsadar rayuwa: Mutanen da suka karɓi taliya sun fi shan wahala — Damagum

“Waɗanda suka karɓi taliya da atamfofi don kawo wannan gwamnati suna jin zafinta fiye da kowa.

Tsadar rayuwa: Mutanen da suka karɓi taliya sun fi shan wahala — Damagum

Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Alhaji Umar Iliya Damagum, ya bayyana cewa ’yan Nijeriya da suka karɓi taliya da atamfa a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2023 sun fi kowa shan wahalar matsin tattalin arziki a halin yanzu.

Damagum ya bayyana hakan ne a lokacin da ya amsa tambayoyin manema labarai a ranar a lokacin ziyarar da ya kai wa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi.

Muƙaddashin  shugaban wanda a cewarsu za kawo cigaba da bunƙasar tattalin arziƙi da kuma jam’iyyar na ƙasa ya kai ziyarar ne a wani ɓangare na ƙoƙarin magance matsalolin da rikicin cikin gidan jam’iyyar.

Damagum ya ce galibin ’yan Nijeriya suna ci gaba da fuskantar wahalhalu sakamakon manufofin Shugaba Bola Tinubu na Jam’iyyar APC.

A cewarsa, “Jam’iyyar APC ba ta da wani shiri na gudanar da mulki, to ta yaya kuke tsammanin wani alheri zai fito daga gare su?

“Waɗanda suka karɓi taliya da atamfofi don kawo wannan gwamnati suna jin zafinta fiye da kowa.

“Kuma wannan ya kamata ya zama darasi ga dukkanmu cewa ya kamata mu nemi gaskiya, mutanen da aka tabbatar za su iya mulki kuma an gwada su, waɗanda suke shirye su yi mulki su ya kamata mu zaɓa,” in ji Damagum, wanda ya ce ’yan Nijeriya suna koyon darasi mai daci.

Damagun, wanda wani ɓangare na Kwamitin Ayyuka na Kasa (NWC) na Jam’iyyar PDP tare da Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa, Samuel Anyanwu, suka dakatar bisa zargin rashin biyayya ga jam’iyyar, ya zargi wasu ’yan Nijeriya da makanta ta hanyar karɓar kayan abinci a lokacin da za a zaɓi Shugaba Bola Tinubu.