Tsadar rayuwa: Kwana da yunwa ya zama jiki ga ’yan Nijeriya — Atiku

Atiku ya koka kan yadda tsadar rayuwa ta zama babban ƙalubale ga iyalai da dama, yana mai cewa farashin man fetur, sufuri da magunguna ya kai matsayin da mutane kaɗan ne kawai ke iya ɗauka.

Tsadar rayuwa: Kwana da yunwa ya zama jiki ga ’yan Nijeriya — Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya ce ƙarancin abinci ya zama wani ɓangare na rayuwar yau da kullum ga miliyoyin ’yan Nijeriya.

Atiku ya koka kan yadda tsadar rayuwa ta zama babban ƙalubale ga iyalai da dama, yana mai cewa farashin man fetur, sufuri da magunguna ya kai matsayin da mutane kaɗan ne kawai ke iya ɗauka.

Ya ƙara da cewa gonaki da dama sun lalace, kasuwanni sun zama kufai, kuma kwana a yunwa ya zame wa mutane da yawa jiki a ƙasar da har yanzu ba ta iya tabbatar da tsaron al’ummarta ba.

A cewarsa, har yanzu dimokuraɗiyya ba ta kawo walwala ga mafi yawan ’yan Najeriya ba.

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wani taron tattaunawa na Ranar Dimokuraɗiyya da Kwamitin Coalition Political Action Committee (COPAC) ya shirya a Abuja.

Ya ce wasu ’yan siyasa sun kauce wa manufofi da ƙa’idojin waɗanda suka yi gwagwarmaya tare da sadaukar da rayukansu domin tabbatar da dimokuraɗiyya a ƙasar.

Atiku ya kuma ce duk da cewa ana gudanar da zaɓe lokaci zuwa lokaci, kusan kashi 70 cikin 100 na ’yan Nijeriya ba su yarda cewa abin da suka zaɓa ake ba su, ko kuma suna ba su damar sauke shugabanni marasa ƙwarewa ba.

 

Ya ce cibiyoyin dimokuraɗiyya da aka kafa domin kare jama’a suna ƙara zama kayan danniya a kansu. A cewarsa, siyasa tana gudana sosai, amma babu ingantaccen shugabanci.

Ya zargi masu mulki da yin watsi da tsarin riƙon amana, yana mai cewa cin hanci da rashawa ya yi ƙamari, yayin da son kai da muradun wasu tsirarun mutane ke barazana ga haɗin kan ƙasa.

Atiku ya ce cibiyoyi da tsarin dimokuraɗiyya suna ci gaba da raunana, yayin da matsalar tsaro ta mayar da wasu sassan ƙasar wuraren da ake fama da kashe-kashe, zubar da jini.

Ya ce ana ci gaba da kashe ’yan Najeriya a kullum, yayin da dakarun soji da jami’an tsaro ke fuskantar nauyi mai yawa, kuma suna buƙatar ƙarin tallafi, ingantattun manufofi da isassun kayan aiki domin shawo kan matsalar.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi alƙawarin cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jam’iyyar ADC za ta kawo ƙarshen matsalar tsadar rayuwa ta hanyar ɗaukar matakan gaggawa da za su inganta rayuwar ’yan Nijeriya masu aiki tukuru.

Ya ce gwamnatin ADC za ta tabbatar da wadatar abinci tare da magance matsalar rashin ƙarin albashi ta hanyar aiwatar da manufofi masu ma’ana da kuma cikin wa’adin da aka tsara.