Tsadar Shanu Na Shirin Hana Fawa A Abuja

Muddin gwamnati ba ta tallafa wa mahauta da bashin sana’a ba, to lallai muna gaf da hakura.

Tsadar Shanu Na Shirin Hana Fawa A Abuja

Tsadar shanu ta tasamma hana sana’ar fawa a Babban Birnin Tarayyar Najeriya Abuja.

Wani mahauci ya bayyana cewa tsadar shanu ta cinye riba har ma ta taba uwar kudin a harkar tasu.

Mahautan sun bayyana cewa duk da yadda suka tsawwala farashin kilon nama, ba su samun wata riba in aka kalli abin da idon basira.

Haka shi ma wani mahauci mai suna Godwin, ya shaida wa Aminiya cewa, “muddin gwamnati ba ta tallafa wa mahauta da bashin sana’a ba, to lallai muna gaf da hakura, domin babu abin da ba mu yi ba saboda mu ga muna samun riba amma abin ya gagara.”

Ana iya tuna cewa, a kwanakin baya Aminiya ta ruwaito cewa an koma amfani da awara maimakon nama a miya a Abuja.

Wannan na zuwa ne a lokacin da al’ummar Musulmi ke gudanar da ibadar azumin watan Ramadan.

Wani magidanci ya bayyana cewa, a da gidansa a watan azumi yana sayen kilo uku na nama domin bararrakawa a yi buɗa baki amma yanzu abin ya ci tura.

Ya ce, ya yi niyyar sayen kayan ciki amma da ya je kasuwar haka ya dawo bai iya saye ba saboda tsadar naman.

’Yan Najeriya dai na ci gaba da ɗanɗana kuɗarsu sakamakon tsadar kayayyakin amfani da masana suka alaƙanta da cire tallafin man fetur da karyewar darajar Naira a matsayin sila.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume