Tsadar shinkafa: Sarkin Musulmi da Gwamna Tambuwal sun bukaci a bude iyakokin kasa

Sakamakon tsada da halin kunci da talakawan kasar nan suke ciki, Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar da Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal su yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta janye dokar da ta sanya na hana shigowa da shinkafa a kasar nan. Sarkin Musulmin ya kuma ya ja kunnen Hukumar Kwastam […]

Tsadar shinkafa: Sarkin Musulmi da Gwamna Tambuwal sun bukaci a bude iyakokin kasa
Tsadar shinkafa: Sarkin Musulmi da Gwamna Tambuwal sun bukaci a bude iyakokin kasa

Sakamakon tsada da halin kunci da talakawan kasar nan suke ciki, Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar da Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal su yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta janye dokar da ta sanya na hana shigowa da shinkafa a kasar nan.
Sarkin Musulmin ya kuma ya ja kunnen Hukumar Kwastam kan ta daina lalatawa ko kone kayan abincin da jami’anta suke kwacewa daga mutane, inda ya ce maimakon yin haka gara su raba kayan ga talakawan kasa mabukata. “Duk kayan da ake amfani da su gara a raba su ga jama’a bai wai ku lalata ba,” inji Sarkin Musulmin.
Sarkin Musulmin ya yi wadannan kalamai ne a ranar Litinin da ta gabata a lokacin da ya karbi Shugaban Hukumar Kwastam ta kasa Kanar Hameed Ibrahim Ali (mai ritaya) wanda ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa da ke birnin Sakkwato.
Sarkin Musulmi ya karfafa maganarsa da cewa: “Ku bude kan iyakokin kasar nan na kasa domin saukaka wahalar da talakan Najeriya ke ciki, yin haka da kyakkyawar manufa da son samun sauki ga talaka haka ne bukatata, za mu dade ba mu samu biyan bukatar da muke so ba matukar abinci yana wahala a wannan yanayin da muke ciki na rufe iyakokinmu, talaka zai ci gaba da  ji a jikinsa, amma ku bar kan iyakokin a bude, abinci ya samu talaka ya yi farin ciki domin sauki ya samu. Mu da ke kusa ga talakawa muna shan koke-koke kan matakin da gwamnati ta dauka na rufe kan iyakokin. Ku bude su tare da sanya ido a rika shigowa da kayan amfani ga jama’a hakan zai kawo saukin wahalar da ake ciki.”
Alhaji Sa’ad Abubakar ya jinjina wa hukumar kan kokarinta na hana shigowa da miyagun makamai da kayan da ba su dace ba zuwa cikin kasar nan, da kuma mayar da martabar aikin da shugaban ya yi.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga Hukumar Kwastam ta dubi yiwuwar canja wasu ka’idojinta ta yadda za su taimaka wa talaka wajen rage radadin mawuyacin halin da yake ciki na tsadar abinci.
Gwamnan ya yi kiran ne a lokacin da Kanar Hamid Ali da tawagarsa suka kai masa ziyara a gidan gwamnatin Jihar Sakkwato. “Ina da yakinin cewa ka san mawuyacin halin da kasar nan take ciki don haka ina kira gare ka koyaushe a rika sa ka’idojin da za su yi sassauci ga jama’a,” inji Gwamna Tambuwal.
Gwamna Tambuwal ya ce saboda dokar hana shigowa da shinkafar ta iyakokin kasa, ya sa ba kowa ke iya sayen ta ba, don haka ya roki a sassauta hana shigowa da ita a iyakokin kasa har sai ya zamanto kasar ta iya noma shinkafar da za ta ishe ta.
Gwamna Tambuwal ya yaba wa kokarin da Kanar Hamid Ali yake yi na sanya tarbiyya ga ma’aikatansa, ya ce kada ya yi kasa a gwiwa a kokarin da yake yi har sai an samu karin kudin shiga ga Najeriya, inda ya ba da tabbacin goyon bayasa ga hukumar.
Kanar Hameed Ali ya kai ziyara Sakkwato ne domin jajanta wa iyayen Shu’aibu Gwadabawa wanda jami’an Kwastam suka kashe a kwankian baya.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe