Tsadar Siminti: Majalisa ta ba Dangote da BUA wa’adi su bayyana a gabanta

Majalisar ta kuma gayyaci Ministan Ma’adanai, Dele Alake, da ya gurfana gaban kwamitin bayan ya kasa bayyana a ranar Talata.

Tsadar Siminti: Majalisa ta ba Dangote da BUA wa’adi su bayyana a gabanta

An bai wa kamfanonin simintin Dangote Cement da BUA da IBETO da sauransu wa’adin kwanaki 14 su gurfana a gaban kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Wakilai domin amsa tambayoyi game da tsadar siminti a Najeriya.

Hakan ya biyo bayan gazawar da kamfanonin suka yi wajen halartar zaman binciken da kwamitin yi gudanar ranar Talata.

Kwamitin haɗin gwiwar wanda ya ƙunshi kwamitocin majalisar mai kula da ma’adanai da kasuwanci da masana’antu da ayyuka na musamman, majalisar ta kafa shi ne domin binciken ƙarin farashin siminti a Najeriya ba da kamfanonin suka yi.

Majalisar ta kuma gayyaci Ministan Ma’adanai, Dele Alake, da ya gurfana gaban kwamitin ranar Talata 19 ga Mayu, 2024, bayan ya kasa bayyana a Talatar nan.

Ta kuma ba da umarnin cewa kamfanin simintin Dangote da BUA da IBETO da sauransu za su bayyana a ranar Litinin, 20 ga Mayu, 2024.

Shugaban kwamatin na haɗin gwiwa wanda kuma shi ne shugaban kwamitin kula da ma’adanai, Ɗan Majalisar Wakilai, Jonathan Gaza Gefwi, ya yi tir da yadda kamfanonin suka yi watsi da gayyatar da aka yi musu, ya ce abin da suka yi na nuni ne da rashin sanin halin da ’yan Nijeriya ke ciki.

A jawabinsa na buɗe taron tun da farko, Gefwi ya bayyana cewa, bitar farashin siminti a wasu ƙasashe kamar Kenya, Indiya da Zambia a shekarar 2021 kaɗai ya nuna cewa Najeriya ce ta fi kowacce ƙasa farashin siminti.

Ya ce, “Farashin siminti a Najeriya ya zarce na Indiya da kashi 69 cikin 100, ya fi na Kenya da kashi 29%, sannan ya wuce na Zambiya da kashi 39%.

“Don haka akwai buƙatar mu taru mu gano dalili, domin kawo sauki ga ’yan ƙasa tare da kare masu zuba jari baki ɗaya.

“Damuwarmu ita ce duk ’yan kasuwa musamman kamfanonin siminti a Najeriya su bunƙasa tare da cimma manufofinsu da da biya bukata ga jama’a ta hanyar da za ta iya samar da ci gaba.”

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja