Tsadar Siminti: Masu bulo sun shiga yajin aiki a Kano

kungiyar Masu Yin bulo reshen Jihar Kano (Kano State Concrete Block Makers and Allied Product Association) ta bayar da sanarwar shiga yajin aiki na gargadi na mako daya don nuna damuwarta kan tashin gwaron zabo da kudin siminti ya yi a kasar nan.Da yake zantawa da maneman labarai a ofishinsa, Shugaban kungiyar, Alhaji Umar Faruk […]

Tsadar Siminti: Masu bulo sun shiga yajin aiki a Kano
Tsadar Siminti: Masu bulo sun shiga yajin aiki a Kano

kungiyar Masu Yin bulo reshen Jihar Kano (Kano State Concrete Block Makers and Allied Product Association) ta bayar da sanarwar shiga yajin aiki na gargadi na mako daya don nuna damuwarta kan tashin gwaron zabo da kudin siminti ya yi a kasar nan.
Da yake zantawa da maneman labarai a ofishinsa, Shugaban kungiyar, Alhaji Umar Faruk Musa ya ce shiga yajin aikin da kungiyar ta yi ya zama wajibi saboda rashin gamsuwa da karin kudin simintin da kamfanonin siminti suka yi.
Ya kara da cewa “Tun daga lokacin da aka yi karin kudin man fetur da dangoginsa masu sana’ar bulo a kasar nan muke gudanar da sana’armu ba kamar yadda muka saba ba, mun ci gaba da gudanar da sana’ar ce don kawai ba mu son mu dakatar da ita, wanda hakan yake nufin korar kimanin mutum dubu 150 a jihar nan daga aiki. Zan iya dukan kirji in ce a duk kayayyakin da ake sayarwa bulo ne kadai ba a kara masa kudi ba, domin an kai shekara hudu farashin siminti yana nan bai canja ba, domin muna sayar da bulo inci tara a kan  Naira 120, shi kuma inci shida da inci hudu da rabi muna sayar da su a Naira 120.”
Ya ci gaba da cewa: “To amma muna cikin wanann hali sai muka wayigari da labarin cewa kamfanonin siminti sun yi karin Naira 600  a kan kowane buhun siminti, wanda ba a taba samun irin wanann kari ba a lokaci guda a kan siminti ba.”
Har ila yau, kungiyar ta ce matukar ba a cimma wata yarjejeniya ba, to akwai yiyuwar karin kudin bulon a jihar, don haka kungiyar ta yi kira ga abokan cinikinta su yi hakuri da halin da suka tsin ci kansu wanda suke fatan warwarewa cikin kankanen lokaci.
Wani mai sana’ar bulo da Aminiya ta tattauna da shi mai suna Abdulalhi Hassan Gandu ya ce suna goyon bayan yajin aikin dari bisa dari, bisa lura da irin wahalhalun da suke fuskanta da za su iya cewa suna aikin ne kawai ba tare da samun riba ba.
“Muna goyon bayan wanann yajin aiki, kasancewar mun dade muna fuskantar matsala ta rashin samun riba a cikin sana’ar nan, muna fata hakan zai kawo mana mafita,” inji shi.
A makon jiya ne Kamfanin Siminti na dangote da sauran kamfanonin siminti suka kara kudin simintinsu daga Naira 1700 zuwa Naira 2300 wanda hakan yake nufin an samu karin Naira 600 a kan kudin buhu siminti.