Tsadar taki: Manoman Kano sun koma amfani da gishiri da kanwa

Hakan dai na da alaka da tsadar taki a bana

Tsadar taki: Manoman Kano sun koma amfani da gishiri da kanwa

Musa Saidu, wani manomi da buhunan takinsa

Tsadar kayan aikin noma a ta fara tilasta wa manoman Kano samar da sababbin hanyoyin da za su bi don yin noma bana a jihar, kamar yadda lamarin yake a akasarin yankunan Arewa.

Binciken da Aminiya ta gudanar ta gano cewa takin zamani da sauran kayan noma sun yi tashin gwauron zabo idan aka kwatanta da bara.

Wannan ya sa manoma suka fara lalubo wasu hanyoyin gwajin wasu sababbin hanyoyin amfani da takin gargajiya da kuma hanyar hada takin zamani da gishiri da kanwa.

Amma masana sun yi gargadi game da irin mummunan illar da hakan zai haifar na dogon lokaci a kan kasa.

Wani manomi a kauyen Yatsi da ke karamar Hukumar Bichi mai suna Musa Sa’idu mai shekara 32, ya ce duk da cewa a baya suna amfani da takin gida, amma ya kasance a matsayin wani tallafi ne ga takin zamani, amma a wannan karon dole sai sun yi amfani da takin gida gaba daya bayan sun hada shi da gishiri da kanwa.

“A wannan karon, mun dogara ne da takin gargajiya a madadin takin zamani saboda ba za mu iya saye ba. Abu kadan da muke samu daga gonakinmu ba zai ishe mu, mu sayi takin ba, balle a samu abin da ake kashewa idan za mu yi amfani da taki. A gaskiya ba ma da kudin, amma kamar yadda kuka sani, wannan ya shafi manoma na gida da kananan ne kawai.

“Na shuka waken soya da dawa a wata gona, da wake da gero a wata gona, amma sai na yi amfani da takin gida duk a gonakin.

“Tun farko, kafin in yi shuka na tara takin dabbobi da toka na zuba a gona. Kuma daga baya, na sayi kanwa, wadda za a gauraye da takin yuriya dan kadan.

“Ba ma amfani da kanwa kawai, muna hada ta da takin zamani na yuriya. Amma a wannan karon, na ga manoma da yawa wadanda ma ba za su iya yin hakan ba; sai dai kawai su zuba kanwar kadai a gonakinsu.

“Ba zan iya bambance yabanyar da za a samu ba, a tsakanin amfani da biyun, amma mun fi tabbas game da taki. Don haka, mun san cewa hatsinmu zai yi girma, amma za mu jira mu ga amfanin da za mu samu,” inji shi.

Wani manomi, Hassan Sani na Rijiyar Zaki a karamar Hukumar Ungogo, ya ce tsadar taki a bana ta sa ya koma bin duk wata hanyar da ta zo masa.

“Ban tava amfani da su ba a baya wato gishiri da kanwa, amma tabbas zan yi amfani da su a bana. Wani da na amince da shi ya gaya min cewa yana aiki sosai idan ka hada shi da taki kadan, da gishiri da kanwa.

“Na riga na sayi gishiri da kanwa, da zarar na samu wasu kudi zan sayo kari saboda ya yi arha, kuma sun ce yana aiki yadda ya kamata.

“Taki ba na matalauta ba ne; kuma ga takin gida, amma saboda tsadar mota ba za ka iya biya a kai maka shi gona ba. Idan wannan gishirin da kanwa sun yi aiki, na san rahamar Allah ce Ya kawo mana kawai,” yadda shaida wa Aminiya.

Shi ma wani manomi Munkaila Gamadan mai shekara 45, daga karamar Hukumar Kura, cewa yin amfani da takin gida ya zama dole a wannan daminar domin ba dukkansu ba ne suke iya sayan taki.

Ya ce mutane da dama sun rage girman gonakinsu saboda tsadar taki, kuma takin yana da wahalar samu.

“Na gaji noma daga kakannina kuma na shafe tsawon shekaruna a cikinsa tun lokacin da na girma.

“Iyayenmu sun yi amfani da takin gida wajen noma, wanda mu ma muka gada, amma sannu a hankali, mun koyi yadda za mu yarda da canje-canje kuma muka koma amfani da takin zamani. Amma a wannan daminar, ya wuce matakinmu; shi ya sa muka yanke shawarar koma wa takin gida,” inji shi.

Sai dai Gamadan ya ce duk da cewa takin gida na da saukin kudi, wadanda suke iya sayen takin zamanin har yanzu suna amfani da shi.

Ya ce ko takin gidan ma yana da wahalar samu domin ana bukatarsa sosai a yanzu.

Ya ce babban kalubalen takin shi ne yadda za a kai shi gonar. A cikin gona inda ake bukatar buhu biyu na takin zamani, dole ne a yi amfani da akalla karamar motar na takin gargajiya.

“Sannan shi kansa takin ya yi tsada. Abin da kawai muke samun kyauta shi ne sharar da ake zubarwa a kan hanyoyi ko wasu wurare. Hatta takin dabbobi ana sayarwa.

“Wasu daga cikinmu za su dogara da takin gida ne kawai, amma zan zuba takin zamani a gonar shinkafata in dogara ga sauran taki domin ba zan iya sayan taki ga dukkansu ba. Ina da gero da dawa da wake da tumatur da albasa da dankali da sauransu,” inji shi.

A yi taka-tsantsan don kauce wa illa – Masana

Duk da cewa amfani da wannan hanya ta gishiri da kanwa abin kirki ne a wurin manoman, to amma masana sun yi gargadin cewa hakan na iya yin illa na dogon lokaci.

Farfesa Ijasini John Tekwa na Sashen Kimiyyar kasa na Jami’ar Tarayya da ke Wukari, ya ce zuba gishiri a madadin taki tamkar kara gishiri ne ga wani rauni domin sinadarin sodium ya riga ya yi yawa a cikin kasa

Ya ce, “Bai kamata a yi amfani da gishiri ba, saboda yawancin amfanin gonakinmu ba sa bukatarsa. A maimakon haka su zuba taki. Noma a yanzu yana jujjuya kwayoyin halitta saboda yana da alaka da muhalli; ba ya lalata muhalli, kuma ba ya haifar da varna ga kasa.

“Hasali ma idan aka zuba takin shanu ko na bola a gona, ba wai kawai za su kara kayan abinci kadai ba ne, har ma suna inganta yanayin kasar.”

Dokta Bassam A. Lawan na Sashen Kimiyyar kasa a Jami’ar Bayero Kano (BUK) shi ma ya yi nuni akan irin illar da za a samu a nan gaba, wadda za ta yi illa ga kasa da kuma manomi.

Ya ce, “Zai yi illa ga samar da kasa saboda zai haifar da matsalar gurvata a cikin kasa, ta yadda wasu abubuwan da suka dace da kasar ke bukata ba za su samu cikin lokaci ba.”

Ya ba da shawarar a yi amfani da takin gargajiya in ba za a samu na zamani ba. Ya ce, “Mafi alheri ga manoma shi ne su yi kokarin yin wani nau’i na takin gida na musamman. Misali, manoma za su iya sa takin da suka saba kaiwa gonakinsu kawai ya zama takin zamani, wato takin zamani, amma adadin sinadarai da ake fitarwa da shi ya zarce na taki.

“Abin da ya kamata manomi ya yi shi ne, ya rufe wannan taki yayin da yake ajiye shi a zuba ruwa a ciki ta yadda zai haifar da wani zafi; wani matakin abin da ke ciki.

Wasu kananan kwayoyin cuta za su yi aiki a kan kayan, ta haka ne za su saki abubuwan gina jiki a cikin nau’i mai yawa ga tsire-tsire ta yadda a karshen rana, manoma za su iya kai takin zuwa gonarsu maimakon daukar taki na yau da kullum.

Yana da alaka da muhalli kuma ba ya da sinadarai. Yana da kwayoyin halitta kuma kowa zai iya amfana,” inji shi.

Wani masani kan amfanin gona a Jami’ar Bayero a Kano, Dokta Aminu Fagge, ya ce duk da cewa taki ma yana da illa ga shuka da muhalli, yawan sinadarin sodium da potassium da ke cikin gishiri da kanwa zai fi illa.

Ya ce cakuduwar ba za ta iya bai wa shukar abubuwan gina jiki da ake bukata ba a tsarin rayuwarta.

Ya kuma shawarci a rika amfani da takin zamani maimakon wannan hanyar da manoma suka dauka.

Hakazalika, shugaban Cibiyar Kula da Abinci ta Najeriya reshen Jihar Kano, Alhaji Auwal Musa Umar, ya ce takaita shuka ga sinadarin sodium da potassium, wadanda wasu ne daga cikin sinadarai masu yawa da kasa ke bukata, zai haifar da “rashin daidaito a cikin kasa da kuma shafar ingancinta.”

“Muna ba su shawarar su yi amfani da takin kashin shanu ko dabbobi ko kuma takin zamani. Za a iya amfani da shara a zaman taki, in ban da leda,” inji shi.

Daga Aminu A. Naganye da Zaharaddeen Y. Shuaibu, Kano da Muhammad Aminu Ahmad