Tsadar takin zamani ta bude wa masu kashin shanu kofa a Gombe

A kullum sama da matasa 30 suke samun aikin yi waje dura takin dabbobin a buhuna.

Tsadar takin zamani ta bude wa masu kashin shanu kofa a Gombe

Wasu manoma a gona

Ganin yadda takin zamani ke neman gagarar manoma saboda tsada, a bangaren takin gargajiya kasuwa ta bude wa masu sayar da kashin shanu a mayankar Gombe inda manoma suke tururuwar sayen takin dabbobin.

Aminiya ta ziyarci mayankar garin Gombe (Kwata) inda ta gano cewa, farashin takin dabbobin ma ya yi tashin gauron zabo da ninki biyu a daidai wannan lokacin da aka fara shiga damina.

Wakilinmu ya gano cewa, manoma daga ciki da wajen garin Gombe kan yi tururuwa zuwa mayankar don neman kashin shanu a matsayin takin da za su kai gonakinsu.

Yanzu haka buhu mai girman kilo 100 na kashin shanu akan sayar da shi kan Naira 2,000 maimakon Naira 1,000 kafin shigowar damina. Ana sayar da buhun takin zamani mai girman kilo 50 a kan Naira dubu 18, zuwa Naira dubu 25, hakan ya danganta da ingancinsa alhali a baya akan sayar da shi kan Naira dubu 10, kafin zuwan damina.

Masu sayar da kashin shanun a kwatar sun danganta tsadar kashin shanun ne da yadda manoma ke nemansa saboda ba sa iya sayen takin zamanin saboda ya yi tsada.

Malam Dan’asabe Audu, shi ne Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Takin Dabbobi a Kwatar Gombe ya ce, yadda ake neman kashin shanun ya sa a wasu lokuta ake nemansa a rasa.

Dan’asabe, ya ce akalla a kullum suna fitar da buhu 50 zuwa 70 na kashin shanun daga kwatar zuwa gonaki a ciki da wajen Gombe.

“Muna kai kashin shanun garuruwa daban-daban a wasu sassan kasar nan musamman Saminaka a Jihar Kaduna da Jos a Jihar Filato da sauran jihohi,” inji shi.

Ya kara da cewa, saboda yadda ake neman takin, yanzu haka sun dauki matasa da yawa da suke aikin dako suna durawa a buhuna saboda masaya.

A cewar Dan’asabe a kullum sama da matasa 30 suke samun aikin yi waje dura takin dabbobin a buhuna.

Shi ma Malam Abdulhamid Mohammed, Sakataren Kungiyar Mahauta ta Gombe ya bayyana kasuwancin takin dabbobin a matsayin babbar hanyar samun kudi inda mutane da yawa suka shiga harkar.

Ya ce, wadansu masaya da suke zuwa daga sassan kasar nan don sayen kashin shanun suna saya har da da kasusuwa da kahonnin shanun suna tafiya da su.

Sakataren ya ce, yana jin dadin yadda abin da aka dauka a matsayin shara kan samar musu da kudi ya bai wa dimbin matasa aikin yi.

Ya ce, kashin shanun bai da illa ga kasar noma kuma yana taimaka wa manoma wajen samun amfanin gona mai yawa.

Wani matashi da ke leburancin dura kashin shanun a buhuna mai suna Adamu Kulani, mai shekara 22 ya ce, a kowace rana yana samun Naira 2000 a aikin.