Tsaf ’yan ta’adda za su iya sace Buhari —Naja’atu

Fitacciyar ’yar siyasar nan ta Jihar Kano, Hajiya Naja’atu Muhammad, ta ce ’yan ta’adda za su iya sace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, duba da yanayin tabarbarewar tsaro a Najeriya.

Tsaf ’yan ta’adda za su iya sace Buhari —Naja’atu

Hajiya Naja’atu Muhammad

Fitacciyar ’yar siyasar nan ta Jihar Kano, Hajiya Naja’atu Muhammad, ta ce ’yan ta’adda za su iya sace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, duba da yanayin tabarbarewar tsaro a Najeriya.

Hajiya Naja’atu, wacce a baya suke dasawa da Shugaba Buhari ta bayyana hakan ne a wata hira da Sashen Hausa na Rediyo Faransa (RFI) ya yi da ita.

Jigon hirar dai shi ne barazanar ’yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna cewa za su yi garkuwa da Shugaba Buhari da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da wasu manyan jami’an gwamnati.

Ta ce, “Me zai hana su dauke shi tunda har suka je suka sami ayarin motocinsa?”

’Yar siyasar ta furta wadannan kalamai ne yayin da take bayar da amsa ga tambayar da aka yi mata a kan ko ’yan ta’addar ba za su iya aiwatar da barazanar da suka yi ba, bayan sojoji sun hana kai musu kudin fansa.

Ga yadda hirar ta kasance:

RFI: Shin kin ga wannan bidiyo?

Najaatu: E, na gani.

To me idonki ya gani?

Yana dada tabbatar da cewa kasar nan babu hukuma, idan dai har wadannan yaran, wadannan ’yan ta’addar za su iya fidda bidiyon kuma a ce mana duk sojojin Najeriya, NIA din Najeriya, DSS din Najeriya, duk tiriliyoyin da aka ce ana kashewa saboda tsaro a Gwamnatin Buhari wai ba ma za su iya gane gun da suke ba…

Duk abubuwan da suka kashe biliyoyi na daloli da aka ce an kashe, wajen sayen makaman tsaro duk karya ake [yi]. Ba sa son matsalar tsaron nan ta kare, sun fi son a ci gaba da rashin tsaron nan don a ci gaba da sace kudin al’umma.

Ya za a yi a ce gwamnati ta kasa gane ina ma aka yi? Yau wata uku da wani abu su kuma har suna ma da wato kaurin idon da za su kalubalanci Shugaban Kasa? Ai sun kalubalance shi tunda har suka kai hari ga ayarin motocinsa.

’Yan Arewa mun shiga uku, mun shiga bala’i da ba wanda zai iya fidda mu yanzu sai Allah saboda Buhari ba shi da niyyar gyarawa.

RFI: Kin ji barazanar da wadannan ’yan bindigar suka yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da [Gwamnan Jihar Kaduna] Nasiru El-Rufai, anya wata rana ba za su kai musu hari ba?

To ai maganar ita ce ba an kai wa ayarin motocin Shugaban Kasa din hari ba, El-rufai bai kwashe ’ya’yansa ya raba su da Kadunan ba?

KAi yanzu rashin tsaron da gaske ne za su iya dauke Shugaban Kasar in dai wadannan jami’an tsaron ne wadanda shi ya gina ya dora, to tabbas za su iya dauke shi.

Me zai hana su dauke shi tunda har suka je suka sami ayarin motocinsa? Ko da ba ya ciki an riga an karya shi, an nuna tun daga sama har kasa kamar yadda yake cewa din ba tsaro, za su iya dauke shin.

Bayan Shugaban Kasa, su kansu ministocin da suke kula da harkokin tsaro tare da hafsoshin tsaron kasa suna da tambabyoyin da za su amsa.

A’a, to ai wa ya dora su a gurin idan dai da cewar mutum idan ka ga ba zai iya ba ka cire shi, ka kawo wani koda kullum kwanan duniya ne a rika canjawa to za a samu daidai.

Amma tsakaninka da su tsakaninmu da jami’an tsaro in ka ga jami’in tsaro a Najeriya to ya zo ya cuce ka ne.

Shi kuma Buhari tsakaninsa da su, su ce ga abin da za a ba su na kudi ya ba su; babu ruwansa da cewa an aikata ko ba a aikata ba, me aka yi da kudin nan babu ruwansa, bai damu ba.

Kuma cuwa-cuwa ce ake yi da wadannan kudaden tsaron; tun daga sama har kasa cuwa-cuwa ake yi.

Yanzu abin da ke faruwa kowanne ya dauko aikin kowanne, soja ya dauki aikin dan sanda, abin da ya kamata a yi wa dan sanda kwata-kwata ba wanda ake yi masa.

Soja wane bincike ya iya, kisa kawai ya iya; to sai dai ya yi ta kashe wanda bai kamata ya kasea ba. Ba horo an kwashe kudaden, in ka duba makaman da ’yan sandanmu suke da su sai kai musu kuka.

To hakan kasar za ta ci gaba?

Naja’atu: To idan dai ’yan Najeriya suka yarda haka za ta ci gaba, ai sarkin yawa ya fi sarkin karfi, idan ’yan Najeriya suka ce ba su yarda ba dole a canja.

To amma munafunci a Arewar nan da kwadayi [sun] hana kowa ya ce komai.

To yau ga shi an wayi gari an ce min akwai wani tsohon gwamna da aka kama, to ka ga duk abin da ke zagaye a cikin gida sai ya dawo gida, ai za ku bar mulkin.

Tunda dai za a kaiwa motocin Shugaban Kasa hari har a jikkata wasu to ai karya ta riga ta kare Buhari ba zai iya ba.

Abin dariya

Amma a martaninsa kan barazanar, Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana shi matsayin abin dariya.

Ya bayyana haka ne a martaninsa bayan wasu ’yan Majalisar Dattawa sun yi barazanar tsige Shugaba Buhari idan har bai magance matsalar tsaro a Najeriya ba.

Ya shaida wa ’yan jarida cewa, “Wadannan kalamai na ’yan ta’addan ba komai ba ne illa shirme da kuma farfaganda.”

Sannan ya ce, shugaban kasa na sane da abubuwan da ke faruwa kuma ana shirye-shiryen daukar matakan da suka dace domin ko a ranar Alhamis majalisar Tsaro ta Kasa za ta zauna kan al’amarin.

Minista ya kuma tabbatarwa da al’umar kasa cewa ba a zaune suke ba, “ Muna yin duk abin da ya kamata mu yi don ganin samar da tsaro a kasar nan.”

Ya kuma kwantar wa da al’umma hankali da cewa kowa zai gani a kasa, kan irin matakan tsaro da gwamnati za ta dauka wanda ba sai ya bayyana ba.

Tabarbarewar tsaro

A baya-bayan nan mastalar tsaro ta addabi yankin Arewacin Najeriya, inda a birnin Tarayya Abuja, wani harin ’yan ta’adda ya sa aka rufe Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya da ke Kwali a ranar Litinin.

A ranar Lahadi da dare kuma ’yan ta’adda sun kashe sojojin rundunar da ke tsaron shugaban kasa a wani harin kwanton bauna.

Sojojin sun gamu da ajalinsu ne a hanyarsu ta dawowa daga Makarantar Koyon Aikin Lauya da ke Bwari, inda suka je gudanar da binciken sharar fage da daukar matakan tsaro bayan ’yan ta’adda sun aike wa hukumar makarantar wasikar barazanar hari.

Daga baya dai an dauke gudanar da bikin yaye sabbin lauyoyi da aka gudanar ranar Laraba daga harabar makarantar zuwa Sakatariyarta da ke yankin Jabi.

Bayan yawon wasu rahotanni da ke cewa Abuja na fuskantar barazanar hari daga ’yan ta’adda, Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, ya ce an dauki duk matakan tsaro da suka dace domin tabbatar da aminci.

Ya kuma yi barazanar tsarewa da hukunta jita-jitar.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos