Tsaftace sana’a yana taimakawa wajen jawo jama’a -Hajiya Rashidah
Wata mai sana’ar dafa abincin sayarwa a garin Benin Jihar Edo mai suna Hajiya Rashidatu Adamu ta shawarci ‘yan uwanta, musamman mata masu dafa abincin sayarwa dangane da batun tsafta game da sana’arsu da ma sauran al’amuran da ke kewaye da su a harkokinsu na yau da kullum, domin su sayar wa jama’a a kasuwa […]
Wata mai sana’ar dafa abincin sayarwa a garin Benin Jihar Edo mai suna Hajiya Rashidatu Adamu ta shawarci ‘yan uwanta, musamman mata masu dafa abincin sayarwa dangane da batun tsafta game da sana’arsu da ma sauran al’amuran da ke kewaye da su a harkokinsu na yau da kullum, domin su sayar wa jama’a a kasuwa ko a gidajensu, duk domin kare lafiyar al’umma.
Hajiya Rashidatu, wadda ta yi wannan tsokaci a wata zantawa da ta yi da Aminiya a shagonta da ke daura da babban titin Aduwawa, Benin, ta jaddada muhimmancin tsafta ne ganin yadda take da tasiri wajen taimaka wa kyakkyawan zaman mutum da al’ummar da ke kewaye da shi.
Ta ce tsaftar jiki da muhalli babban al’amari ne a rayuwar dan Adam, lamarin da ya bambanta shi da dabba, wadda ita ma kanta takan fi samun lafiya da yalwa, idan ana tsaftace ta a yayin da ake kiwonta. “Lallai ne mu tsaftace sana’armu a cikin gida ne ko a kasuwa. Saboda haka ina kira tare da shawartar mata ’yan uwana da suke sana’a irin wadda nake yi ta dafa abincin sayarwa ga jama’a da cewa mu tsaftace ta ko ta wane juyi, ya kasance duk abin da za mu yi amfani da shi wajen gudanar da abincin, kamar ruwa da abin da za mu yi amfanin da shi na dafa abincin ko raba shi, ko aiwatar da shi, duk mun tsaftace shi kafin mu yi amfani da shi”.
Hajiya Rashidatu ta ce, “Ita wannan sana’a ta sayar da abinci, akwai albarka da rufin asiri a cikint, don haka kulawa da ita yana kara mata armashi ga jama’a. Na tabbatar duk wata mai irin wannan sana’ar ta dafa abinci na sayarwa tana taimaka wa jama’a ne kuma akwai albarka tare da samun lada a wurin Ubangiji, don haka muddin mai wannan sana’ar tana kulawa da tsaftace abincinta da muhallinta gaba daya, to lallai kowa zai yi sha’awar ya saya ya ci hankali kwance, akasin idan da tana kazanta ne”.