Tsaftar Muhalli: Gwamnatin Kano ta kama Naburaska
Mustapha Naburaska, daya daga cikin fitattun jaruman dandalin Kannywood, a karshen makon da ya gabata ya fada komar kwamitin tsaftar muhalli da Gwamnatin Kano ta kafa. Jarumin wanda mazauni ne a Unguwar Tudun Wada ta Karamar Hukumar Nasarawa da ke Birnin Dabo, ya tsinci kansa a gaban kotun tafi-da-gidanka bayan ya keta dokar kwamitin tsaftar […]
Mustapha Naburaska, daya daga cikin fitattun jaruman dandalin Kannywood, a karshen makon da ya gabata ya fada komar kwamitin tsaftar muhalli da Gwamnatin Kano ta kafa.
Jarumin wanda mazauni ne a Unguwar Tudun Wada ta Karamar Hukumar Nasarawa da ke Birnin Dabo, ya tsinci kansa a gaban kotun tafi-da-gidanka bayan ya keta dokar kwamitin tsaftar muhalli wadda ta hana fita har sai karfe 10.00 na safiya a duk ranar Asabar ta karshen kowane wata.
- Yadda muka fara wasan kwaikwayo a Masana’antar Kannywood – Dandolo
- Yadda ’yan Kannywood suka yi jimamin rasuwar Sarkin Zazzau
- Yadda ’yan Kannywood suka yi jimamin rasuwar Sarkin Zazzau
Naburaska yayin zantawa da manema labarai na Gidan Rediyon Freedom, ya ce rashin sani ya sanya ya fito domin halartar wata jana’iza kuma a yanzu ya fahimci cewa tsaftar muhalli ta kore kowane uzuri.
Kotun ta nemi Jarumin ya biya naira dubu biyar a matsayin tarar keta dokar zama a gida domin tsaftace muhalli inda ya nemi rangwami kuma ta yi masa sassaucin biyan naira dubu uku.