‘Tsagaita wutar’ ke nan?
A ranar 17 ga watan Oktoba, 2014 Babban Hafsan Tsaro Cif Aled Baded ya fitar da sanarwar cewa gwamnatin tarayya ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ’yan kungiyar Boko Haram a Saudiyya. Ya fitar da sanarwar ne bayan taron tattaunawar da ta shafi sha’anin tsaro ta kwana uku tsakanin Najeriya da kuma Kamaru. […]
A ranar 17 ga watan Oktoba, 2014 Babban Hafsan Tsaro Cif Aled Baded ya fitar da sanarwar cewa gwamnatin tarayya ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ’yan kungiyar Boko Haram a Saudiyya. Ya fitar da sanarwar ne bayan taron tattaunawar da ta shafi sha’anin tsaro ta kwana uku tsakanin Najeriya da kuma Kamaru.
“Mun yi tattaunawa ta kwana uku tsakaninmu da Kamaru, ba kuma tare da tsana ko fargaba ba, ina sanar wa jama’a gwamnatin tarayya ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da kungiyar Jama’atu Ahlus Sunnah Lid Da’awati Wal Jihad wadda aka fi sani da Boko Haram, don haka ina ba manyan hafsoshin soja da ke fagen daga umarnin biyayya ga wannan yarjejeniyar.”
Jama’a da dama sun kadu, wasu sun yi mamaki, wadansu sun bayyana shakkunsu, wadansu kuma sun amince da batun yarjejeniyar, hakan ya faru ne lokacin da jama’a suka fidda rai wajen kawo karshen rikicin, musamman ma da aka shafe shekara biyar ana rikici, inda dubban jama’a suka rasa rayukansu, tattalin arziki ya gurgunce a yankin Arewa maso Gabas, sannan dubban jama’a suka yi gudun hijira, sannan miliyoyi suke cikin fargaba, sai ga shi an ce rikicin ya kusa zama tarihi. Bayan nan a ranar 20 ga Oktoba, 2014 aka samu rahoton cewa za a sako ’yan matan Chibok da aka sace tare da yin garkuwa da su tun a watan Afrilu, 2014. kasashen duniya sun bayyana farin cikinsu sakamakon wannan rahoton, inda Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce wannan labarin na farin ciki ne, ba kuma tun yanzu ya kamata a sako ’yan matan ba, “Boko Haram sun ce za su sako ’yan matan, sannan mun samu labarin nan da wadansu awowi ko kwanaki za a sako su.” Inji shi a lokacin da yake jawabi yayin taron Hukumar Bunkasa Tattalin Arzikin kasashen Turai.
Babban Daraktan Hukumar NOA kuma Kodinetan Cibiyar Sadarwa ta kasa, Mista Mike Omeri ya ce ’yan matan Chibok suna cikin koshin lafiya da kuma kwanciyar hankali. Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin jama’a, Dokta Doyin Okupe, ya ce yarjejeniyar ta samu nasara ne sakamakon huldar diflomasiyya da ta hada da Nijar da kuma Chadi, ko Gwamna Jihar Barno Kashim Shettima gwamnan da ya fi fama da rikicin Boko Haram ya bayyana jin dadinsa, “wannan mataki ne mai kyawu da ya kamata a ba shi goyon baya.”
Sai dai wadansu awowi bayan an bayyana cim ma yarjejeniyar sai ’yan Boko Haram suka kai hari a wadansu garuruwan da ke Jihar Barno, sun kuma kai hare-haren ne sansanin sojoji. Shaidu daga bangaren sojojin sun ce ’yan Boko Haram sun kawo hare-haren ne da manyan makamai, makaman ma sun fi wadanda suke amfani da su a da.
Za a gane girman matsalar ne a idan aka lura da yadda ’yan Boko Haram suka kwace Mubi, gari mafi girma na biyu a bangaren kasuwanci a Jihar Adamawa. Sun canza sunan Mubi zuwa ‘Madinatul Islam’, inda a ranar Talata kuma suka kwace kamfanin siminti na Ashaka da ke Jihar Gombe.
Sannan an ga bidiyon Shekau yana karyata batun yarjejeniya tsakaninsu da gwamnatin tarayya, sannan ya rufe duk wata kofar da za ta haifar da yarjejeniya a gaba.
Wata taswira da wata jarida ta fitar dangane da batun rikicin Boko Haram din, ta nuna yadda Boko Haram suka kwace iko da fadin kasar da ya yi daidai da fadin kasar wadansu jihohi uku na Kudancin Najeriya.
Wannan babban al’amari ne da yake neman fin karfin gwamnati, inda duk da cewa an sanya dokar-ta-baci yanzu tsawon shekara biyu a Jihar Barno da Yobe da kuma Adamawa, inda aka jibge dubban sojoji a jihohin, amma an kasa kawo karshen rikicin. Tun farkon rikicin gwamnatin Jonathan ta ce wadansu ’yan Arewa ne suka kirkiro rikicin ne don su hana Jonathan tsayawa takara a shekarar 2015, a idanun kasashen duniya kuma suna kallon gwamnatin Jonathan a matsayin ko dai ba ta da niyyar kawo karshen rikicin, ko kuma ta gaza, ko ma duka, yanzu al’ummar kasar sun shiga cikin halin ha’ula’i.
Abin tambaya yanzu shi ne, shin wa ya yaudari gwamnati har ta fitar da sanarwa cim ma yarjejeniyar tsagaita wutar? Ko dai an fitar da sanarwar ce saboda jami’an gwamnati da na tsaro ba su da hanyar da za su kawo karshen rikicin? Duk da al’amarin na kara ta’azzara amma gwamnati tana ci gaba da cewa an har yanzu ana ci gaba da tattaunawa don kawo karshen rikicin, ba tare da kuma sun yi bayanin takamaiman halin da ake ciki ba, kowace rana dai akwai batutuwan jan kafa da gwamnati take zuwa da su a matsayin uzuri wajen kawo karshen rikicin, inda ’yan Boko Haram ke ci gaba da kwace garuruwa, wanda hakan ke nuna bakar wahalar da gwamnati za ta sha kafin ta mayar da Najeriya turbar da take.