Tsagerun Neja-Delta: Gwamnati ta yi sulhu da su ko ta bi da karfin soja?

A ’yan kwanakin nan ne aka samu wasu tsageru da suke tada kayar baya a yankin Neja-Delta, suna tayar da bama-bamai ga rijiyoyin mai da ke yankin da nufin gurgunta tattalin arzikin kasa. Abin tambaya a nan shi ne, wace hanya ya kamata gwamnati ta bullo masu? A hau teburin sasanci da sulhu da su […]

Tsagerun Neja-Delta: Gwamnati ta yi sulhu da su ko ta bi da karfin soja?
Tsagerun Neja-Delta: Gwamnati ta yi sulhu da su ko ta bi da karfin soja?

A ’yan kwanakin nan ne aka samu wasu tsageru da suke tada kayar baya a yankin Neja-Delta, suna tayar da bama-bamai ga rijiyoyin mai da ke yankin da nufin gurgunta tattalin arzikin kasa. Abin tambaya a nan shi ne, wace hanya ya kamata gwamnati ta bullo masu? A hau teburin sasanci da sulhu da su ko kuwa a fito masu ta karfin soja? Ga abin da wakilanmu suka kalato daga mutane daban-daban:

A bi su ta karfin tsiya –Bello Jega

Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja

Alhaji Bello Maikano Jega: “Ni dai a ra’ayina dangane da wadannan mutane ’yan tawayen Neja-Delta, kamata ya yi gwamnati ta bude masu wuta, a yi maganinsu ta karfin tsiya, domin kuwa lalama ba za ta yi masu ba. Ya kamata dai mu fahimta da cewa kasar nan dai ba ta kabila ko yanki daya ba ce. Shi kuma man fetur da suke gadarar ana hakowa a yankinsu, ba mallakinsu ba ne su kadai, hakkin kowane dan kasa, na kowane yanki ne. Haka kuma da dukiyar Arewa ta noma da kiwo aka yi amfani tun da farko aka hako man fetur din. Don haka abin da suke yi karya doka ne, kuma bai kamata a sanya masu ido ko kuma a ce za a rarashe su ba, domin kuwa ba su cancanci haka ba.”

Kada a yi sulhu da su – Abdulwahab Birnin Gwari

Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja

Abdulwahab Sani Birnin Gwari: “Ya kamata Gwamnatin Najeriya ta yi wa tsagerun Neja-Delta shiri na musamman, ta yadda za a darkake su, kamar yadda ake yi wa ’yan Boko Haram. Ni ban goyi bayan a ce za a yi sulhu ko a bi su ta lalama ba, domin kuwa ai da farko an neme su ta lalama suka kiya, suka ci gaba da kai hare-hare ga dukiyar kasa. Lallai Najeriya ba tasu ba ce su kadai, domin kuwa dukiyar da ke yankinsu ta kasa ce, ta al’umma ce gaba daya. Bai kamata a ce za a sakar masu fuska ba tun da farko, domin idan aka ce za a yi sulhu da su, nan gaba ma kowa zai iya daukar makamai ya fara yakar gwamnati da nufin a yi sulhu da shi. Najeiya ta fi karfin wata kabila ko wani yanki daya.”

Sulhu ya kamata a yi da su – Hassan Ningi

Hamza Aliyu, a Bauchi

Abdulmumini Hassan Ningi: “Abin da zan fada game da ’yan Neja-Delta masu tayar da kayar baya shi ne, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta yi sulhu da su domin babu abin da ya kai zaman lafiya muhimmanci a rayuwa, duk da cewa har yanzu suna ci gaba da fasa bututun mai a yankin. Ina tabbatar maka da cewa matukar suka ci gaba da fasa bututun mai, karshe matsalar sai ta shafi dukkan jihohin Najeriya, domin za a fuskanci matsalar rashin kudin da za a biya ma’aikata albashi. Ya kamata su fahimci cewa da kudin noman auduga da gyada aka tono man da suke tunkaho a kai, yanzu suna wannan tada kayar baya ne domin yanzu dan Arewa ne yake mulki a Najeriya. Wajibi ne gwamnati ta dauki mataki kamar yadda aka ci lagon ’yan Boko Haram a Arewa, su ma da sannu za su zamo sai tarihi. Bana goyon bayan a bude musu wuta amma ina goyon bayan a yi sulhu da su sannan kuma gwamnati ta gudanar da bincike ta ina suke samun manyan makaman da suke amfani da su. Marigayi tsohon Shugaban kasa Janar Sani Abacha ya taba cewa duk wata kungiyar ta’addaci da aka gagara murkushe ta cikin sa’o’i 24, to tabbas akwai manyan da suke daure mata gindi da makamai.”

Tattaunawa ya kamata a yi da su – Nuhu Zaki

Hamza Aliyu, a Bauchi

Abdulrazak Nuhu Zaki: “Abin da zan fada game da ’yan Neja-Delta shi ne, ya kamata Gwamnatin Tarayya ta fara tattaunawa da ’yan kungiyar Neja-Delta masu fasa bututun mai a kudancin kasar nan, idan aka ce za a murkushe su da karfi, ba mu san abin da zai biyo baya ba. A matsayina na wanda ya shugabanci jama’a a mataki daban-daban dole a fahimci cewa suna da daurin gindi daga wasu kasashen waje wadanda suke ba su manyan makamai suke amfani da su. Rashin tattaunawa ne ya haifar mana da kungiyar Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabas. Kafin su yi karfi sai da masana suka ce a tattauna da su amma aka ki daga bisani suka yi karfin da ya wuce misali, sai da lokaci ya kure gwamnati ta nemi yin sulhu da su lokaci kuma ya kure. Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dage sosai wajen tattaunawa da sarakunan yankin da gwamnoninsu da sauran masu ruwa da tsaki a yankin, domin shawo kan matsalar na fasa bututun mai da kungiyar take ci gaba da yi. Ba na goyon bayan a murkushe su da karfi, domin ba mu san wane irin shiri suka yi ba. Idan ka ji makaho yana cewa a yi wasan jifa watakila ya taka dutse ne, tabbas akwai kasashen Turawa da ba su kaunar zaman lafiyar Najeriya. Watakila su ke rura wutar fitinar a bayan fage.”

Kada a yi sulhu da su – Idris Bature

Umar Rayyan, a Kaduna

Idris Bature: “A gaskiya ni ba na goyon bayan a yi sulhu da su, ya kamata a dauki mataki sosai a kansu saboda su ba mutane masu kaunar zaman lafiya ba ne. Ka ga wannan shugaban namu, mutum ne mai son zaman lafiya, saboda sai da zaman lafiya ake samun ci gaba da wanzuwar arziki.”

Sulhu ba zai yiwu ba – Musbahu Zariya

Umar Rayyan, a Kaduna

Musbahu Zariya: “Kamar yadda na ga an yi zama da su da Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, hujjojin da suka ba da, da kuma bukatun da suka gabatar masa, abin zai yi wahala. Saboda haka nake ganin idan an zauna da su da wuya a samu cin ma wani sulhu.”