Tsakanin abinci da magani wanne ya fi muhimmanci ga dan Adam?

Abinci da magani, abubuwa ne masu matukar muhimmanci ga rayuwar bil Adama, amma abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu, wanne ne ya fi muhimmaci ga rayuwar mutum? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu: Abinci ya fi muhimmanci – Alasan Musa Musa Kutama, a Kalaba Alasan Musa Mai Jallabiya: “A gaskiya […]

Tsakanin abinci da magani wanne ya fi muhimmanci ga dan Adam?
Tsakanin abinci da magani wanne ya fi muhimmanci ga dan Adam?

Abinci da magani, abubuwa ne masu matukar muhimmanci ga rayuwar bil Adama, amma abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu, wanne ne ya fi muhimmaci ga rayuwar mutum? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

Abinci ya fi muhimmanci – Alasan Musa

Musa Kutama, a Kalaba

Alasan Musa Mai Jallabiya: “A gaskiya abinci zan iya cewa ya fi muhimmanci ga dan Adam fiye da magani saboda shi abinci dole a neme shi. Magani kuwa ba kowa ba ne kodayaushe yake da bukatarsa.”

Magani bai kai abinci ba – Muhammad Tasi’u

Musa Kutama, a Kalaba

Muhammad Tasiu Auwalu: Abinci ya fi muhimmanci saboda haka ne ma ko wace rayuwa ba ta yi sai da abinci. Saboda gaskiya dole sai an ci za a rayu, ita dai cuta ba koda yaushe ake yin ta ba. Shi kuma abinci ya zama dole sai lallai ka ci za ka rayu, sanna magani kuma sai mutum ba shi da lafiya ne zai saurare shi. Abinci kuwa koda lafiyarka kalau, dole ka neme shi.”

Magani ya fi abinci muhimmanci – Aliyu Muhammad

Muhammad Yaba, a Kaduna

Aliyu Muhammad: “Abinci ya fi mahimmanci a jikin dan Adam, domin sai babu abinci rashin lafiya ke faruwa. Rahin abinci shi ke kawo rashin lafiya kuma mutum yana iya daurewa na tsawon kwanaki bakwai kana rashin lafiya ko zazzabi ba ka sha magani ba amma zai yi wuya ka dauki kwanaki bakwai ba ka ci abinci ba. Wannan ne ya sa na ce abinci ya fi mahimmanci.”

Ko a asibiti abinci ya fi – Abdullahi Musa

Muhammad Yaba, a Kaduna

Abdullahi Musa: “Abinci ya fi amfani ga dan Adam saboda koda asibiti mutum ya je sai likita ya tambaye shi ko ya ci abinci, kafin a ba shi magani ko allura. Kai, akwai maganin da ma ba za ka sha ba sai ka ci abinci; in ba haka ba kuwa sai ya yi wa mutum illa. Saboda haka abinci ya fi muhimmanci ga jikin dan Adam.”

Abinci na gaba da magani – Muhammad Auwal

Adam Umar, a Abuja

Muhammad Auwal Sani: “Abinci ya fi magani muhimmanci, dalili kuwa shi ne ai maganin kansa musamman allura, ba a amfani da shi sai an ci abinci. Idan kuwa a ka yi amfani da shi haka nan ba tare da an ci abinci ba, to halakarwa zai yi a maimakon amfanarwa cikin hanzari da aka san maganin zamani da shi.”

Abinci ya fi amfani ga dan Adam – Bilyaminu Isa

Adam Umar, a Abuja

Sunana Bilyaminu Isa: “A gaskiya abinci ya fi muhimmanci fiye da magani, kuma koda asibiti ka je ba su yarda su ba ka magani sai ka ci abinci. Sannan idan mutum yana bin ka’idar abincinci koda rashin lafiya ya yi jikkatar da zai yi masa ba zai kai na wanda ke sake da cin abinci ba.”