Tsakanin aikin albashi da sana’ar hannu wanne ya fi rufin asiri?
A garin neman abinci, mutane sun bambanta. Wasu suna yin ayyukan gwamnati ko na kamfani, inda ake biyan su albashi duk wata. Wasu kuwa sana’ar hannu suke yi, yadda suke dogaro da abin da suke samu yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne, tsakanin wadannan hanyoyin neman abinci, wanne ya fi samar da […]
A garin neman abinci, mutane sun bambanta. Wasu suna yin ayyukan gwamnati ko na kamfani, inda ake biyan su albashi duk wata. Wasu kuwa sana’ar hannu suke yi, yadda suke dogaro da abin da suke samu yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne, tsakanin wadannan hanyoyin neman abinci, wanne ya fi samar da rufin asiri? Ga abin da mutane ke cewa:
Sana’a ta fi aikin albashi – Ibrahim Musa
A.A.Masagala, a Benin
Alhaji Ibrahim Musa Wamako: “A ganina, lamari ne da ya zama kowa da abin da ya fahimta a ciki na sha’anin rayuwa, domin shi mai aiki yana karbar albashi na wata-wata da shi ya dogara; idan wata ya kai karshe zai samu albashinsa shi kuma mai sana’a matukar ya ci gaba da wannan sana’ar to lallai zai ci gaba da samun abin rufin asiri cikin sauki da kwanciyar hankali. Don haka duk da cewa ni ba mai karbar albashiba ne amma a fahimtata, mai sana’a ya fi rufin asiri fiye da mai karbar albashi nesa ba kusa ba. Domin ba kasafai ba ne da za a samu mai karbar albashi da ba a bin sa bashi na rabin albashinsa ko ma fiye da hakan. Daga wannan za a gane cewa mai sana’a ko da karama ce ya fi mai albashi rufin asiri.”
Babu abin da ya fi sana’a – Sadik Dauda
A.A.Masagala, a Benin
Malam Sadik Dauda: “Ni abin da na fahimta shi ne, babu abin da ya fi sana’a rufa wa mutum asiri, domin ita sana’a a ciki za ka samu ka ci da kanka da kuma iyalinka ba sai ka shiga wani yanayi ko karbar kayan mutane da sunan bashi ko rance ba. Amma albashi yana da matsala, domin a wani lokacin za a samu jinkirin biya ya kai watanni mai karbar albashin bai samu an biya shi ba. Kun ga daga nan fallasa ta fara, babu maganar biyan bukata a kan kari ballantana rufin asiri, domin ta wannan halin idan ba mai hakuri ba ne; idan ya sake bashi sai ya hau ya cinye duk abin da zai samu na watannin har ya nunka. Don haka ni a ganina, sana’a ta fi albashi rufin asiri da biyan bukata.”
Sana’a ko kasuwanci ya fi albashi – Alhaji Ahmadu
Nasiru Bello, a Sakkwato
Alhaji Ahmadu: “Kasuwanci ya fi rufin asiri. Dalilina a fadin haka kuwa shi ne, shi mai albashi yana da tsari da shiri a kowane wata wanda ba zai yarda ya tsallake wannan ba, don ya san iya kudinsa, sabanin mai kasuwanci ko sana’a da a kullum ubangijinsa ne kawai ya san adadin abin da zai iya samu na kudi a kasuwancinsa. Misali, ni a yanzu ina da mata hudu da ’ya’ya 29, mata da maza. A kullum ni ke biya musu bukatunsu daidai gwargwado. Nakan kula da su yadda ya kamata. Wannan rufin asiri sai kasuwanci. Ka dubi makamancina a aikin gwamnati, mai difiloma ke nan, kana ganin in ba wata kujera yake samanta ta zalunci ba, yana iya rike irin iyalina kuma ya biya musu bukatunsu daidai gwargwado, har ya taimaki wasu kamar yadda nake yi?”
Rufin asiri sai kasuwanci – Nura Bodinga
Nasiru Bello, a Sakkwato
Nura Badinga: “Ni ma’aikacin gwamnati ne amma na tabbata rufin asiri na wurin kasuwanci, saboda duk wani ma’aikaci da ka sani a wurin dan kasuwa ya dogara; nan yake karbar bashi har karshen wata ya biya. Amma ka taba ganin dan kasuwa ya je neman bashi wurin ma’aikacin albashi? Da dan kasuwa da ma’aikaci za su je karbar bashi, dan kasuwan zai riga samu kuma shi za a fi aminta da zai kawo kudin nan kan lokaci. Natsuwar dan kasuwa ba ta zama daya da ma’aikaci don shi baya gudun kora ko kwairi ko dakatarwa ko bincike, yana iya sanya duk rigar da yake so ba tare da an tuhume shi ba, al’amuransa ba a zargin su.”
Rufin asiri sai sana’ar hannu – Umar Dogo
Aliyu Babankarfi, a Zariya
Umar Dogo Tudun Jukun Zariya: “Sana’ar hannu ta fi rufin asiri, komai kankantar jari, musamman idan akwai abokan hulda. Dalilina kuwa shi ne, shi ma’aikacin wata sai wata ya kare za a ba shi hakkinsa, sannan ya biya bukatunsa. Shi kuwa mai sana’ar yau da kullum, duk lokacin da ya fita zai samu abin biyan bukata, har ma ya rage kuma shi ya fi tabbas a kan samun halal, musamman idan ya tsare gaskiya. Shi kuwa mai aikin wata idan ba mai tsoron Allah ba ne, za ka ga albashinsa kafin wata ya kare sun kare a bashi, sai mai cuwa-cuwa kawai ke kai labara. Don haka sana’ar yau da kullum t afi rufin asiri.”
Aikin albashi kashin kare ne – Shugaba danmaliki
Aliyu Babankarfi, a Zariya
Shugaba danmaliki: “Ai ba a hada tsakanin ma’aikacin wata da mai sana’ar hannu ko kasuwanci. Dalili kuwa shi ne, idan mai sana’ar hannu ya rike amana kuma ya tsare gaskiya to sai ya fi mai aikin wata cin halal, domin shi da basirarsa ko kuma da karfinsa yake gudanar da sana’arsa. dan kasuwa kuwa idan jarinsa na halal ne, shi ma ka ga kusan kullum sai ya samu abin da zai samu rufin asiri. Ma’aikacin wata-wata kuwa mafiya wayansu ba su cika zuwa aiki ba. In ma sun je sukan tashi ba a kan lokaci ba kuma kashi casa’in cikin dari ’yan cuwa-cuwa ne. Don haka na ce albashin wata kashin kare ne, ba ya taki.”