Tsakanin asibiti da makaranta wanne ya fi muhimmanci ga al’umma?
Makaranta dai wuri ne na koyon ilimi, wanda shi ne gishirin rayuwar duniya, a yayin da kuma asibiti ya kasance wurin neman lafiya ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu wanne ya fi muhimmanci ga rayuwar al’umma, asibiti ko makaranta? Ga abin da wakilanmu suka tataro mana daga ra’ayoyin mutane: Makaranta ta […]
Makaranta dai wuri ne na koyon ilimi, wanda shi ne gishirin rayuwar duniya, a yayin da kuma asibiti ya kasance wurin neman lafiya ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu wanne ya fi muhimmanci ga rayuwar al’umma, asibiti ko makaranta? Ga abin da wakilanmu suka tataro mana daga ra’ayoyin mutane:
Makaranta ta fi muhimmanci – Aminu Abubakar
Aminu Abubakar: “Gaskiya makaranta ta fi asibiti, domin ta hanyar makaranta ce kawai ake samun ilimi. In kuwa babu ilimi da me za a yi aikin asibiti? Shi kansa asibitin ma ai sai ta hanayr makarantar ake gina shi. Hatta magungunan asibiti ma dole sai ta hanayar makarantar ne ake iya gano yadda za a sarrafa su da yadda ake bayarwa. Da wannan dalilai ne nake jawo hankalin masu karatu ko tantama bana yi, makaranta ta fi asibiti.”