Tsakanin asibiti da makaranta wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 1

Makaranta dai wuri ne na koyon ilimi, wanda shi ne gishirin rayuwar duniya, a yayin da kuma asibiti ya kasance wurin neman lafiya ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu wanne ya fi muhimmanci ga rayuwar al’umma, asibiti ko makaranta? Ga abin da wakilanmu suka tataro mana daga ra’ayoyin mutane: Asibiti ya […]

Tsakanin asibiti da makaranta wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 1
Tsakanin asibiti da makaranta wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 1

Makaranta dai wuri ne na koyon ilimi, wanda shi ne gishirin rayuwar duniya, a yayin da kuma asibiti ya kasance wurin neman lafiya ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu wanne ya fi muhimmanci ga rayuwar al’umma, asibiti ko makaranta? Ga abin da wakilanmu suka tataro mana daga ra’ayoyin mutane:

Asibiti ya fi muhimmanci – Auwal Yunusa

Auwal Y. Yunusa: “Asibiti gaskiya a nawa tunani ya fi makaranta muhimmanci, domin komai sai da kafiya za a yi. Da lafiyar za ka iya fita neman ilimin kuma komai iliminka idan ba ka da lafiya sai ka je asibiti likita ya duba ka. Idan akwai ilimi, ba asibiti, wannan duk shirme ne, babu abin da ilimi zai iya yi sai da lafiya. Don haka ni a nawa, asibiti ya fi makaranta.”