Tsakanin asibiti da makaranta wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 2

Makaranta dai wuri ne na koyon ilimi, wanda shi ne gishirin rayuwar duniya, a yayin da kuma asibiti ya kasance wurin neman lafiya ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu wanne ya fi muhimmanci ga rayuwar al’umma, asibiti ko makaranta? Ga abin da wakilanmu suka tataro mana daga ra’ayoyin mutane: Makaranta ta […]

Tsakanin asibiti da makaranta wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 2
Tsakanin asibiti da makaranta wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 2

Makaranta dai wuri ne na koyon ilimi, wanda shi ne gishirin rayuwar duniya, a yayin da kuma asibiti ya kasance wurin neman lafiya ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu wanne ya fi muhimmanci ga rayuwar al’umma, asibiti ko makaranta? Ga abin da wakilanmu suka tataro mana daga ra’ayoyin mutane:

Makaranta ta fi asibiti – Alhaji Lado

Alhaji Lado Mai Gudubale: “A ra’ayina dangane da wanda ya fi muhimmanci a tsakanin makaranta da asibiti shi ne, ai ko ja babu makaranta ta fi asibiti muhimmanci nesa ba kusa ba. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, ai a bayyane yake cewa duk matsayin da dan Adam ya taka don zama wani abu sai da ya je makaranta aka koya masa tukun kafin ma ya kai ga kirkirar wani abu wai shi asibiti. Don haka makaranta ce ke kan gaba fiye da asibiti, domin sai da ilmi ne tukun ake samar da jami’in da zai yi aiki a asibitin, wato likita ke nan.”