Tsakanin asibiti da makaranta wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 3
Makaranta dai wuri ne na koyon ilimi, wanda shi ne gishirin rayuwar duniya, a yayin da kuma asibiti ya kasance wurin neman lafiya ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu wanne ya fi muhimmanci ga rayuwar al’umma, asibiti ko makaranta? Ga abin da wakilanmu suka tataro mana daga ra’ayoyin mutane:Makaranta ce kan […]
Makaranta dai wuri ne na koyon ilimi, wanda shi ne gishirin rayuwar duniya, a yayin da kuma asibiti ya kasance wurin neman lafiya ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu wanne ya fi muhimmanci ga rayuwar al’umma, asibiti ko makaranta? Ga abin da wakilanmu suka tataro mana daga ra’ayoyin mutane:
Makaranta ce kan gaba – Malam Karumi
Malam Karumi Mai Takalma: “Ra’ayina kan abin da ya fi muhimmanci tsakanin makaranta da asibiti shi ne, ai in ana dara fidda uwa ake yi. In ana zancen makaranta ai ba a hada ta da komai, kasancewar ita ce uwa mai ba da mama kan abin da ya shafi ci gaban al’ummar duniya kwata. Domin duk yayin da aka yi maganar makaranta ai tamkar an fadi ci gaban dukkan al’umma ne, domin ita makaranta sai an je ta ne tukun za a samu duk wani ilmi na kirkira. Saboda haka a bayyane yake kan cewar makaranta ita ce ke gaba da komai, domin shi kansa likita mai aiki a asibitin sai da ya je makaranta aka koyar da shi ilmin gane cututtuka kafin ya zama likitan. Ka ga kuwa asibiti ba ya zama asibiti sai da likita ko kuma wani jami’in kiwon lafiya.”