Tsakanin asibiti da makaranta wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 5

Makaranta dai wuri ne na koyon ilimi, wanda shi ne gishirin rayuwar duniya, a yayin da kuma asibiti ya kasance wurin neman lafiya ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu wanne ya fi muhimmanci ga rayuwar al’umma, asibiti ko makaranta? Ga abin da wakilanmu suka tataro mana daga ra’ayoyin mutane: Makaranta ce […]

Tsakanin asibiti da makaranta wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 5
Tsakanin asibiti da makaranta wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 5

Makaranta dai wuri ne na koyon ilimi, wanda shi ne gishirin rayuwar duniya, a yayin da kuma asibiti ya kasance wurin neman lafiya ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu wanne ya fi muhimmanci ga rayuwar al’umma, asibiti ko makaranta? Ga abin da wakilanmu suka tataro mana daga ra’ayoyin mutane:

Makaranta ce farko – Salisu Mai Kananzir

Alhaji Salisu Adamu Mai Kananzir: “Ni a ganina, makaranta ta fi asibiti mahimmanci, domin shi asibitin da ake Magana idan aka gina shi sai an sami makarantar da za a yi karatu kafin a sami wadanda za su je su yi aiki a cikinsa. Haka kawai ba a sami makarantar da za a karantar da ma’aikatan asibiti ba, babu yadda za a yi a gina asibitin. Don haka ni a ganina makaranta ta fi asibiti mahimmanci.”