Tsakanin asibiti da makaranta wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 6

Makaranta dai wuri ne na koyon ilimi, wanda shi ne gishirin rayuwar duniya, a yayin da kuma asibiti ya kasance wurin neman lafiya ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu wanne ya fi muhimmanci ga rayuwar al’umma, asibiti ko makaranta? Ga abin da wakilanmu suka tataro mana daga ra’ayoyin mutane: Asibiti ya […]

Tsakanin asibiti da makaranta wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 6
Tsakanin asibiti da makaranta wanne ya fi muhimmanci ga al’umma? 6

Makaranta dai wuri ne na koyon ilimi, wanda shi ne gishirin rayuwar duniya, a yayin da kuma asibiti ya kasance wurin neman lafiya ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu wanne ya fi muhimmanci ga rayuwar al’umma, asibiti ko makaranta? Ga abin da wakilanmu suka tataro mana daga ra’ayoyin mutane:

Asibiti ya fi makaranta muhimmanci – Auwalu Mai Siminti

Auwalu Sharubutu Mai Siminti: “A gaskiya ni dai a ganina, asibiti ya fi makaranta mahimmanci saboda sai da lafiya za a tafi makaranta. Domin idan aka wayi gari babu lafiya babu yadda za a tafi makaranta. Sannan kuma asibiti shi ne ya kamata a fi ingantawa, musamman a yankunan karkara saboda mahimmancinsa ga rayuwar al’umma. Don haka ni a ganina, asibiti ya fi makaranta mahimmanci.”