Tsakanin ginin gida da noma, wanne ya fi cin rai?

Wadannan al’amura guda biyu, wato noma da ginin gida suna da matukar cin rai ga mutumin da ya sanya su gaba. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu, wanne ya fi cin ran mutum? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga mutane daban-daban: Gini ya fi noma cin rai – Ahmed A. Bagi […]

Tsakanin ginin gida da noma, wanne ya fi cin rai?
Tsakanin ginin gida da noma, wanne ya fi cin rai?

Wadannan al’amura guda biyu, wato noma da ginin gida suna da matukar cin rai ga mutumin da ya sanya su gaba. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakaninsu, wanne ya fi cin ran mutum? Ga abin da wakilanmu suka kalato mana daga mutane daban-daban:

Gini ya fi noma cin rai
– Ahmed A. Bagi

Abubakar Haruna, a Legas

Ahmed A. Bagi: “Gini ya fi noma cin rai saboda ta iya yiwuwa a gidan haya kake kuma an matsa maka ka tashi, ka ga dole za ka rika damuwa ka ga ka kammala ginin ka rufa kun tare da kai da iyalinka a cikin gidan amma shi noma ai abu ne na lokaci, idan ba lokacinsa ba ne ba za ka damu ba sai lokacin yin sa ya zo sannan za ka damu ka kammala.”

Gini ya fi cin rai
– Misis Olafeju

Abubakar Haruna, a Legas

Misis Olafeju: “Gini ya fi noma cin rai saboda gini duk sanda ka fara shi Allah-Allah kake ka ga ka gama shi kuma hankalinka ba zai kwanta ba har sai ka kammala shi amma shi noma ba za ka damu ba saboda ita shukar ai ba kai za ka fito da ita ba, Allah ne zai tsiro da ita. Ka ga dole ka yi hakuri har sai lokacin da ta fito ka girbe.”

Noma yafi aikin gini cin rai – Bob Siriri

Rabilu Abubakar, a Gombe

Malam Abdulkarin Usman (Bob Siriri): “A gaskiyar magana ni a tawa fahimtar, babu yadda za a yi ka hada aikin gini da noma, domin ta kowace hanya noma ya fi gini cin rai. Muddin kana noma, kullum idan ba ka da karfi da zarar damina ta sauka fargabar yadda za ka sami taki kake yi ko yaya za a yi ka iya nome gonarka saboda tsoron awo. Shi noma abu ne da yake da lokaci wanda ba yadda za a yi ka bar lokacinsa ya wuce ba ka yi ba. Ka ga shi gini kuwa koda wane lokaci za ka iya yinsa ba kamar noma ba da yake da lokacin yinsa.”

Aikin gini ya fi noma cin rai – Malam Ya’u Inuwa

Rabilu Abubakar, a Gombe

Ya’u Inuwa: “Ni a nawa ganin, aikin gini yafi noma cin rai saboda shi aikin gini saboda tsabar cin rai da zarar ka fara so kake ka ga sai ka gama, musamman ma ga mai karamin karfi. Noma kuwa za ka iya hakura da gonar ma gaba daya. Ka ga aikin gini idan aka ce Allah Ya hore maka ka mallaki fili, so kake ka ga ka fara tara bulo da yashi har ka kai lokacin da za a ce ka rufe, ka shiga kuma duk abin da ka samu ko nawa ne za ka ga mutum yana kokarin hana cikinsa ya sa kudin wajen gini. Ba lallai ba ne kuma idan kana noma ka iya daurewa ka nome gonar duka, za ka iya nome kadan ka hakura da sauran idan al’amari ya sarke maka kuma za ka iya ma hakura baki daya. Wani ko hawainiya ko maciji ya gani a gonar karshen noman ke nan. Ka ga ashe kuwa noma bai kai gini cin rai ba.”

Gini ya fi cin rai – Sulaiman Zariya

Adam Umar, a Abuja

Sulaiman Abdullahi Zariya: “Ginin gida ya fi noma cin rai. Dalili kuwa shi ne, shi gini wani abu ne wanda sai ka yi mai tanadi sannan za ka yi shi. Hasali ma idan ya riski damina, in ba ka yi shi ka gama ba to hankalinka zai tashi. Shi kuwa noma wani abu ne wanda za ka yi shuka ka sake nomawa amma idan ka ishe ciyawa ta lalata gonar a saboda karancin taki ko wani abu amma ba zai dami mutum sosai ba. Shi ko gini musamman ma idan mutum yana gidan haya sai ya tayar da hankali sosai, har mutum ya gwammace dawowa gidan haka nan ba silin, ba katanga, ya hakura haka nan.”

Ginin gida ya fi noma cin rai
– Sanusi Buros

Adam Umar, a Abuja

Sanusi Buros: “A gaskiya gini ya fi cin rai, dalili kuwa shi ne idan a ka riga a ka fara shi sannan ba a samu damar kammalawa da wuri ba har damina ta zo, sannan ba wani waje, to tashin hankali ne musamman ma idan mutum yana da iyalai. Amma shi ko noma idan ka yi na farko, to kana ma iya barin shi haka nan, kuma ka samu amfani gwargwado, duk da dai ba zai kai irin na gonar da ta samu karin kulawa ba.”