Tsakanin Gwamna Masari da ragwayen ’yan adawa
Ni dai ban ga beken Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ba, wanda shi ne ya bai wa ’yan kasa ’yancin yin magana, wanda dalili ke nan wasu kan bude bakinsu su yi ta zuba ratata kamar ballallen famfo, suna nuna wautarsu a fili, sai daga bisani kuma su gane cewa sun kwafsa.Domin bai wa kowa ’yancin […]
Ni dai ban ga beken Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ba, wanda shi ne ya bai wa ’yan kasa ’yancin yin magana, wanda dalili ke nan wasu kan bude bakinsu su yi ta zuba ratata kamar ballallen famfo, suna nuna wautarsu a fili, sai daga bisani kuma su gane cewa sun kwafsa.
Domin bai wa kowa ’yancin da tsarin mulki ya yi, shi ya sanya Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ya sakar wa kafofin watsa labarai na jihar mara, inda ya bai wa gidajen rediyo da talabijin mallakar jihar umurnin su bai wa kowa damar amfani da su, ba tare da la’akari da jam’iyyar da ya fito ba, su bayyana ra’ayoyinsu, koda kuwa ra’ayoyin nasu ba masu dadin ji ba ne ga gwamnati. Hakan ke nuna cewa gwamnan ya yi amanna da cewa samun adawa mai karfi ke karfafa wa masu mulki su yi abin da ya dace ga al’umma, tare da kiyayewa.
Baya ga wannan dama da gwamna ya ba ’yan adawa, ya kuma fito da tsarin ganawa da al’umma kai tsaye, domin ba kowa damar ba da gudunmowarsa. Kamar yadda ya ce da bakinsa: “Sha’anin mulki wani abu ne da ya kamata a baje a kan tebur, ba a karkashinsa ba, domin mutane su gani da idanuwansu, su bi kadi sannan su tofa irin nasu miyan domin a samun ci gaba.”
Wani karin abin dubawa kuma, gwamna bai gajiyawa da tuntubar masana domin ganin yadda za a ciyar da Katsina gaba. A tsawon mulkinsa na shekara daya, sau hudu ke nan ya gana da duk wani dan jiha da ke da gudunmowar bayarwa, sannan bai bar kowa a duhu ba, na irin kudin shiga na jiha da kananan hukumomi da kuma yadda ake kashe su a jihar. Ko a kwanan nan, an yi irin wannan taron, a kan idanun masu martaba sarakunan Katsina da Daura. Kusan dukkan gwamnonin da suka mulki jihar nan, in ban da guda daya na farar hula, duk sun halarta. Sauran sun hada da tsoffi da sabbin ’yan majalisar tarayya, manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya masu ci da wadanda suka yi ritaya, manyan ’yan kasuwa, manyan ’yan siyasa da duk wani mai fada a ji a kowane fage, ya halarta domin bayar da tasa gudunmowa. Wannan kuwa Masari ya yi haka ne da nufin cika alkawuran da ya dauka a yayin yakin neman zabe.
Na dauki lokaci ne ina wannan bayanin, domin wadanda suka maida sukar Masari sana’arsu su gane cewa kansu suke cuta, kuma suna nuna wautarsu da jahilcinsu a fili. Domin shi Gwamna.
Kamar yadda ya saba kwarmatonsa, Shugaban Jam’iyyar NCP, Malam AbdulMumin Shehu Sani, ya kalubalanci Gwamna Masari da ya “bayyana wa al’umma dukkan kudaden da suka shiga aljihun gwamnatinsa tun daga watan Mayun bara,” inda ya yi ikirarin wai duk da cewa yana da ’yancin a bayyana masa haka a doka amma ya nemi hukumomin da suke da ikon yin haka, amma ba su yi ba. Ni kuwa na ce wannan ikirari na Shugaban NCP Katsina akwai shakku a cikinsa, kasancewar yana daya daga cikin mutanen da gwamna ke gayyata a duk lokacin taron masu ruwa da tsaki wajen gina Katsina, sai dai ba ya halarta kuma ba da wani uzuri ba.
Haka kuma wannan batu nasa ai shifcin gizo ne, kasancewar Ma’aikatar Al’amuran Kudi ta Gwamnatin Tarayya tana wallafa dukkan kudaden da take raba wa jihohi da kananan hukumomin kasar nan, don haka adadin da jihar nan ta samu a tsawon shekara daya ba boyayye ba ne ga kowa. Don haka ga duk mai son sanin adadin kudin, kawai zai shiga shafin ma’aikatar na intanet. Idan kuma bai da kwamfuta, jaridun kasar nan duk sun wallafa, sai kawai ya nema ya gani. Ba ma wannan ba, ai a duk lokacin da gwamna ya zo zauren taron masu ruwa da tsaki na Jihar Katsina, yana bayyanawa karara, adadin kudaden da jiha da kananan hukumomi suka samu da kuma yadda aka kashe su, domin al’umma su tabbatar.
Misali, a taron da ya gabata makonni uku da suka wuce, a Gidan Gwamnati, gwamnan ya bayyana cewa kudaden da kananan hukumomi 34 suka samu a watan Mayu su ne Naira biliyan 2.4, duk da cewa suna bukatar Naira biliyan 3.4 domin biyan albashi da fansho a watan. Wannan ke nuna cewa, kafin kananan hukumomin su iya biyan ma’aikata da malaman makaranta da ’yan fansho, suna bukatar karin Naira biliyan 1.1. Haka labarain ya kasance a watannin baya tun daga Yunin 2015, lokutan da dole sai da gwamnatin jiha ta rika cika gibin Naira biliyan 3.1 kafin su iya biyan albashi da fansho. Sai dai a wannan karon, gwamnatin jiha ba ta da sukunin cika wa kananan hukumomi wannan gibi, domin kuwa kudin shigar da ta samu a watan Mayu, duka Naira biliyan 2.146 ne, inda ake bukatar Naira biliyan 2.234 domin biyan albashi da fansho.
Don haka, a ce Malam AbdulMumin Shehu Sani ya fito ya ce “tantance ma’aikatan kananan hukumomi wai wata manufar Gwamna Masari ce ta kashin kansa” ba kashin gaskiya a ciki, kasancewar gaskiya a bayyane take yadda kananan hukumomin suka kusa durkushewa saboda ma’aikatan jabu da marasa amfani da kuma wadanda ba su cancanta da aiki a nan ba da suka yi yawa. Misali, a karamar hukuma daya, an samu kimanin mutum 20 ’yan wani ‘babban gida’ da suke amsar albashi duk wata, duk da cewa babu wani ma’aikaci a karamar hukumar da zai gaya maka ga aikin da suke yi, ko kuma ya ce maka ya taba ganinsu sun zo aiki, domin kuwa ta banki ake tura musu albashin. Don haka ba za mu yi mamaki ba yadda mutane irin Shugaban NCP na Katsina za su fito suna irin wadannan yasassun maganganu, domin kuwa mafi yawa daga ma’aikatan bogi da ke amsar dukiyar gwamnati, ’ya’ya ne ko ’yan uwa ko matan auren wasu da ake kira da manyan kasa a cikin al’umma.
Shaida a bayyane take yadda Gwamnatin Masari ta samu amsuwa daga dukkan al’ummar jihar. Babban misali shi ne, yadda a kwanakin baya kungiyar kwadago (NLC) reshen jihar ta ki shiga yajin aikin da uwar ta kasa ta kira saboda janye tallafin fetur. Haka kuma kungiyar Likitoci ta Najeriya, reshen jihar ita ma ta ki shiga nata yajin aikin saboda a cewar kungiyar, ta gamsu da mulkin Masari da yadda yake kokarin bunkasa harkar lafiya a jihar. Kwanaki ma har takardar gamsuwa ta aika wa gwamnan, tana yaba masa kan matakan inganta harkar lafiya. Don haka saboda me za mu mayar da hankali ko nuna damuwa da kwarmaton kasassun kuma ragagen ’yan adawa?
Labaran shi ne Babban Jami’i Mai Taimaka Wa Gwamnan Jihar Katsina ta fuskar watsa labarai, [email protected]