Tsakanin hannu da kafa wanne ya fi muhimmanci a jikin mutum?

Allah Ya halitta mutum cikin kyakkyawar siffa, sannan Ya yi masa gabobi da sassa daban-daban masu amfani ga rayuwarsa ta yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka dauki hannu da kafa, wanne ya fi mahimmanci da amfani a jikin mutum? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin mutane daban-daban da suka tafka mahawara kamar […]

Tsakanin hannu da kafa wanne ya fi muhimmanci a jikin mutum?
Tsakanin hannu da kafa wanne ya fi muhimmanci a jikin mutum?

Allah Ya halitta mutum cikin kyakkyawar siffa, sannan Ya yi masa gabobi da sassa daban-daban masu amfani ga rayuwarsa ta yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka dauki hannu da kafa, wanne ya fi mahimmanci da amfani a jikin mutum? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin mutane daban-daban da suka tafka mahawara kamar haka:

kafa ta fi mahimmanci

– Sa’datu Muhammad (5)

Sa’adatu Muhammad: “Duk wadannan abubuwan guda biyu suna da muhimmnci ga rayuwar bil’adama amma kafa ta fi muhimmanci idan ka yi la’akari da yawan amfaninsu, domin kafa kusan duk abin da hannun zai yi za ta taimaka masa amma hannu bai taimakon kafa ta kowace hanya. Abinci bai samuwa ba kafa amma ana cin shi ko ba hannu. Kai abin sha’awa ga kafa shi ne, duk wani aiki da hannu ke yi kafa na yinsa. kafa wata halitta ce babba da Ubangiji Ya yi ma bayiSa, shi ya sa ma duk halittar da aka sani, dabbobi ko tsuntsaye ko tsirrai ko kwari ko mutane da aljannu da makamatansu, duk suna da kafafu amma ba dukkansu ke da hannu ba. Wannan kadai ya isa ka gane kafa ta fi hannu muhimmaci a rayuwar dan Adam.”

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya