Tsakanin hannu da kafa wanne ya fi muhimmanci a jikin mutum? (2)
Allah Ya halitta mutum cikin kyakkyawar siffa, sannan Ya yi masa gabobi da sassa daban-daban masu amfani ga rayuwarsa ta yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka dauki hannu da kafa, wanne ya fi mahimmanci da amfani a jikin mutum? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin mutane daban-daban da suka tafka mahawara kamar […]
Allah Ya halitta mutum cikin kyakkyawar siffa, sannan Ya yi masa gabobi da sassa daban-daban masu amfani ga rayuwarsa ta yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka dauki hannu da kafa, wanne ya fi mahimmanci da amfani a jikin mutum? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin mutane daban-daban da suka tafka mahawara kamar haka:
Hannu ya fi kafa – Abubakar Zubairu
Abubakar Zubairu: “Ai a gaskiya ba sai an fada ba, hannu ya fi kafa muhimmanci domin akwai guragu da suke amfani da hannaye a madadin wasu abubuwa da kafa ke yi. Amma zai yi wuyar gaske kafa ta iya yin ayyukan da hannaye ke yi, amma hannaye suna iya gudanar da kusan dukkan abubuwan da kafafu ke yi. Ka ga ke nan hannaye sun fi kafafu muhimmanci da amfani ga rayuwar dan Adam.”