Tsakanin hannu da kafa wanne ya fi muhimmanci a jikin mutum? (3)

Allah Ya halitta mutum cikin kyakkyawar siffa, sannan Ya yi masa gabobi da sassa daban-daban masu amfani ga rayuwarsa ta yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka dauki hannu da kafa, wanne ya fi mahimmanci da amfani a jikin mutum? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin mutane daban-daban da suka tafka mahawara kamar […]

Tsakanin hannu da kafa wanne ya fi muhimmanci a jikin mutum? (3)
Tsakanin hannu da kafa wanne ya fi muhimmanci a jikin mutum? (3)

Allah Ya halitta mutum cikin kyakkyawar siffa, sannan Ya yi masa gabobi da sassa daban-daban masu amfani ga rayuwarsa ta yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka dauki hannu da kafa, wanne ya fi mahimmanci da amfani a jikin mutum? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin mutane daban-daban da suka tafka mahawara kamar haka:

 

Hannu ya fi kafa amfani a jikin mutum – Lawal Muhammad

Lawal Muhammad Katsina: “Hannu ya fi kafa amfani, domin duk mutumin da bai da hannu babu yadda za a yi ya gudunar da wasu aikace-aikacensa yadda ya kamata, domin a wannan zamani da muke ciki ko sana’a za ka yi dole sai da hannu za ka yi ba da kafa ba. Ko wajen kirga kudi ko sarrafa wasu sassan jiki, dole da hannu za ka yi ba da kafa ba. Idan mutum ya rasa hannu za a iya kiransa miskini amma kafa ba za ta sa a kira shi miskini ba. Misali, yau idan kana da kafa ba ka da hannu ko sana’ar zaune ba za ka iya ba amma idan kana da hannu ba ka da kafa, a zaune za ka iya duk wata sana’a kuma ka dogara da kanka.”

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya