Tsakanin hannu da kafa wanne ya fi muhimmanci a jikin mutum? (4)

Allah Ya halitta mutum cikin kyakkyawar siffa, sannan Ya yi masa gabobi da sassa daban-daban masu amfani ga rayuwarsa ta yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka dauki hannu da kafa, wanne ya fi mahimmanci da amfani a jikin mutum? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin mutane daban-daban da suka tafka mahawara kamar […]

Tsakanin hannu da kafa wanne ya fi muhimmanci a jikin mutum? (4)
Tsakanin hannu da kafa wanne ya fi muhimmanci a jikin mutum? (4)

Allah Ya halitta mutum cikin kyakkyawar siffa, sannan Ya yi masa gabobi da sassa daban-daban masu amfani ga rayuwarsa ta yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka dauki hannu da kafa, wanne ya fi mahimmanci da amfani a jikin mutum? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin mutane daban-daban da suka tafka mahawara kamar haka:

 

kafa ta fi hannu amfani – Isma’il Baba Shamaki

Isma’il Baba Shamaki: “Ni a nawa ra’ayin, kafa ta fi hannu amfani a jikin mutum; domin idan mutum bai da kafa babu yadda zai yi koda abun gudu ne ya faru sai dai a gudu a bar shi amma idan hannu ne mutum bai da shi komai zai iya yi. Duk wanda bai da kafa ya fi fuskantar barazana a rayuwa fiye da marar hannu, domin ko kwatami mutum zai tsallaka idan bai da kafafu sai dai ya shiga ta ciki ya wuce. Muddin ba ka da kafafu ko wajen ’yan uwanka za ka zamar masu jidali, domin komai za ka yi sai dai a yi maka amma marar hannu shi ba haka ba ne.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya