Tsakanin hannu da kafa wanne ya fi muhimmanci a jikin mutum? (5)
Allah Ya halitta mutum cikin kyakkyawar siffa, sannan Ya yi masa gabobi da sassa daban-daban masu amfani ga rayuwarsa ta yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka dauki hannu da kafa, wanne ya fi mahimmanci da amfani a jikin mutum? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin mutane daban-daban da suka tafka mahawara kamar […]
Allah Ya halitta mutum cikin kyakkyawar siffa, sannan Ya yi masa gabobi da sassa daban-daban masu amfani ga rayuwarsa ta yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka dauki hannu da kafa, wanne ya fi mahimmanci da amfani a jikin mutum? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin mutane daban-daban da suka tafka mahawara kamar haka:
kafa ce jigon rayuwa – Zayyanu Dingyadi (4)
Zayyanu Dingyadi: “Ra’ayi riga inji Bahaushe. kafa rayuwa ce ta dan Adam fiye da hannu. A duk lokacin da mutum ya rasa hannu daya, ba a kallon ya tagayyara fiye da wanda ya rasa kafa daya saboda hakan ma mahukunta sun yadda kafa ta fi muhimmanci ga rayuwa fiye da komai, suka fito da tsare mutum a gidan yari bai zuwa ko’ina, a mtsayin babban hukuncin da zai taimaka ya gyara halinsa. Idan mutum ya zauna bai zuwa ko’ina damuwa takan kama shi. Ka dubi tafiyar marar hannu da marar kafa ka ga wa yafi shan wahala a rayuwa? Hannu na da muhimmanci amma kafa ta fi shi muhimmanci. kafa jigon rayuwa, don addini ma yakan nuna hidimarsa da kafa ake yin ta, kamar zuwa masallaci ko jihadi da sauransu.”