Tsakanin hannu da kafa wanne ya fi muhimmanci a jikin mutum?(1)
Allah Ya halitta mutum cikin kyakkyawar siffa, sannan Ya yi masa gabobi da sassa daban-daban masu amfani ga rayuwarsa ta yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka dauki hannu da kafa, wanne ya fi mahimmanci da amfani a jikin mutum? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin mutane daban-daban da suka tafka mahawara kamar […]
Allah Ya halitta mutum cikin kyakkyawar siffa, sannan Ya yi masa gabobi da sassa daban-daban masu amfani ga rayuwarsa ta yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka dauki hannu da kafa, wanne ya fi mahimmanci da amfani a jikin mutum? Wakilanmu sun samo ra’ayoyin mutane daban-daban da suka tafka mahawara kamar haka:
Hannu ya fi amfani – Muhammad Labaran
Muhammed Labaran Musa: “Ni dai a ganina hannaye sun fi kafafu muhimmanci saboda ayyukan da hannaye suke yi sun fi wanda kafafu ke yi yawa. Kuma, akwai mutanen da ake guntile musu kafafu a dalilin wata lalura musamman hadari amma idan suka samu sauki sai ka ga har tukin mota suna yi. Misali, matar da kuka yi bayaninta kwanan baya a shafukan Aminiya, wacce take amfani da kafafunta kawai wajen gudanar da dukkan ayyuka har da sanya kwalli da shafa hoda, ta fadi da bakinta cewa, akwai ayyukan da ba ta iya yi da kafafun nata sai dai wani ya yi mata, kamar shanya suturu da ta wanke.”