Tsakanin hoto da labari, wanne ya fi muhimmanci a cikin jarida?

Labari da hoto, abubuwa ne masu muhimmanci a cikin jarida amma abin tambaya a nan shi ne, tsakanin wadannan abubuwa biyu, wanne ya fi muhimmanci? Wakilanmsu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana: Hoto ya fi muhimmanci – Muhammad Lawal Musa Kutama, a Kalaba Muhammad Lawal Salim Abbas: “Gaskiya a […]

Tsakanin hoto da labari, wanne ya fi muhimmanci a cikin jarida?
Tsakanin hoto da labari, wanne ya fi muhimmanci a cikin jarida?

Labari da hoto, abubuwa ne masu muhimmanci a cikin jarida amma abin tambaya a nan shi ne, tsakanin wadannan abubuwa biyu, wanne ya fi muhimmanci? Wakilanmsu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suka kalato mana:

Hoto ya fi muhimmanci – Muhammad Lawal

Musa Kutama, a Kalaba

Muhammad Lawal Salim Abbas: “Gaskiya a ra’ayina, wanda ya fi mahimmanci, a samu sakon abin da ake so a fadi shi ne hoto. Hoto shi ne zai nuna maka duk abin da yake faruwa. Ka ga shi labari za a iya rubuta abin da ba haka ba ne amma kuma shi saboda muhimmancinsa ya fi labara, ko a makaranta ma idan aka tambaye ka abu ba ka sani ba, za ka iya zana hotonsa. Don haka ni hoto ya fi labari muhimmanci a jarida.”

Labari ya fi hoto – Habibu Adamu

Musa Kutama, a Kalaba

Habibu Adamu: “Labari ya fi mahimmanci a ganina, domin shi labari idan aka buga shi, ka ajiye jaridar shekara 100. Masu zuwa idan ka dauko jaridar labarin na nan hoto kuwa wani ma zai iya karyatawa ko ma kin yarda da shi. Muhimmancin da labari yake da shi a jarida ko kusa ba za a hada shi da na hoto ba.”

Duk suna da muhimmanci – Nura Adamu

Aliyu Babankarfi, a Zariya

Nura Adamu Ofisa: “Labari da hoto a jarida duk suna da muhimmanci, domin idan kuka ba da labari kuma kuka nuna hoto za a fi gamsuwa fiye da a ce labara ne kadai. Misali, labarinku na sa da aka haifa da kai biyu, ga labarin ga hoton. Wani hoton kawai yake so ya gani, domin bai iya karatu ba. Don haka dukkansu suna da muhimmanci a jarida.”

Labari ya fi

muhimmanci – Sama’ila Ibrahim

Aliyu Babankarfi, a Zariya

Sama’ila Ibrahim Bawa: “Labari ya fi hoto muhimmanci ga mai karanta jarida, musamman wanda yake da ilimi amma ga mai koyon karatu to sai a ce hoto ya fi muhimmanci a wurinsu. Labari ai shi ne jarida, musamman labaran da suke fitowa a jarida da wuya ka ji hakan bai faru ba kuma mu a wurinmu, jaridar da ta fito da labarai an fi sayenta fiye da wadda hotuna suka fi yawa a cikinta. Don haka labari ya fi muhimmanci a jarida.”

Labari shi ne kan gaba – Iliyasu Adamu

Muhammad danladi Ibrahim, a Minna

Iliyasu Adamu Albishir: “Magana ta gaskiya game da wannan lamarin shi ne, labari ya fi muhimmanci a jarida fiye da hoto. An gina jarida ne kacokan a kan labara ba hoto ba. Idan aka lura sosai za ka ga cewa jaridu irin Aminiya sun ware shafuka na musamman domin masu karatu su kalla sannan su gina labari da kansu wanda ba lalle ne labarin ya yi daidai da abin da yake hoton ba. Ka ga misali a daya daga cikin hotunan da aka sa na Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso yana magana da wata mata, ba mu san abin da suke tattaunawa a wurin ba. Sannan wani misalin da zan ba ka shi ne na fadan da danmajalisa da direban Gwamna suka yi a kan mace, an gina labarin yadda duk wanda ya karanta zai gamsu, sannan kuma an fahimci wadanda suka aikata wannan lamarin mai matukar daure kai.”

Labari na da muhimmanci – Bawa Dabaci

Muhammad danladi Ibrahim, a Minna

Bawa Dabaci: “Alal hakika, maganar gaskiya labari ya fi muhimmanci fiye da hoto a jarida. Dalilin da ya sa na fadi haka kuwa shi ne, ba kowa zai iya fassara labaran da ke hotuna yadda ya kamata ba, da har zai iya gamsar da jama’a. Muddin aka gina labari yadda ya kamata, zai isar da sakon da jama’a za su fi fahimta. Shi hoto ko hotuna a jarida suna kara wa labarai armashi ne.”