Tsakanin ilimi da kudi, wanne ya fi wahalar nema?1
Tsakanin ilimi da kudi, wanne ya fi wahalar nema? Neman ilimi ya fi neman kudi wahala -Malam Haruna Musa Sunana Haruna Musa: Neman ilimi da neman kudi, abubuwa biyu ne masu matukar amfani a rayuwar dan Adam, saboda suna tafiya ne kafada-da-kafada da juna ganin tun kafin Allah Madaukakin Sarki Ya halicci dan Adam Ya […]
Tsakanin ilimi da kudi, wanne ya fi wahalar nema?
Neman ilimi ya fi neman kudi wahala -Malam Haruna Musa
Sunana Haruna Musa: Neman ilimi da neman kudi, abubuwa biyu ne masu matukar amfani a rayuwar dan Adam, saboda suna tafiya ne kafada-da-kafada da juna ganin tun kafin Allah Madaukakin Sarki Ya halicci dan Adam Ya yi masa kasafin duk abubuwan da zai yi amfani da su a harkokinsa na rayuwarsa daga farko zuwa karshe. Shi kuwa ilimi Allah Ya wajabta mana nemansa yadda Annabi Muhammad [S.A.W] ya jaddada tun yana raye, kuma kowane musulmi ya tabbata iyalinsa da zuriyarsa sun same shi, sabanin arziki. Muddin danka ya samu ilimi, zai samu komai cikin sauki muddin ya yi amfani da shi yadda ya kamata. Zai yi wuya tashi daya ka samu ilimin da zai amfane ka, ba tare da ka wahala ba, amma kudi kam suna iya samunka cikin sauki har kuma zuriyarka su gaje ka. A tawa fahimtar, a takaice, neman ilimi ya fi neman kudi wahala.