Tsakanin ilimi da kudi, wanne ya fi wahalar nema?2
Yau filin muhawara ya kawo tambayar ko tsakanin ilimi da kudi wanne ya fi wahalar nema, kuma mutanen da aka tuntuba sun bayar da gudunmawarsu ne kamar haka: Neman ilimi ya fi neman kudi wahala -Malam Muhammad SanusiSunana Muhammad Sanusi Mai Carbi: A gaskiya neman ilimi ya fi neman kudi. Ilimi ya fi wahalar samu, […]
Yau filin muhawara ya kawo tambayar ko tsakanin ilimi da kudi wanne ya fi wahalar nema, kuma mutanen da aka tuntuba sun bayar da gudunmawarsu ne kamar haka:
Neman ilimi ya fi neman kudi wahala -Malam Muhammad Sanusi
Sunana Muhammad Sanusi Mai Carbi: A gaskiya neman ilimi ya fi neman kudi. Ilimi ya fi wahalar samu, wanda ba ya rasa nasaba da irin amfanin da ya ke yi a rayuwar dan Adam, musamman a al’amuransa na yau da kullum. Kudi babu mamaki, ko ka same su, ba za su wadatar da kai har zuwa karshen rayuwarka ba. Babbar ribar ilimi a ma yadda ni na fahimta, shi ne aiki da shi yadda muke ganin wasu daga cikinmu suna kwatantawa a harkokinsu na kasuwanci, wanda ya sa ala dole wasu ke koyi da su. Ka ga sun samu lada goma da goma ke nan.