Tsakanin ilimi da kudi, wanne ya fi wahalar nema?5
Yau filin muhawara ya kawo tambayar ko tsakanin ilimi da kudi wanne ya fi wahalar nema, kuma mutanen da aka tuntuba sun bayar da gudunmawarsu ne kamar haka: Kudi ya fi ilimi wahalar nema -Aminu SalisuNi Aminu Salisu ina ganin kudi ya fi ilimi wahalar nema saboda shi ilimi kana iya samunsa a gidanka, amma […]
Yau filin muhawara ya kawo tambayar ko tsakanin ilimi da kudi wanne ya fi wahalar nema, kuma mutanen da aka tuntuba sun bayar da gudunmawarsu ne kamar haka:
Kudi ya fi ilimi wahalar nema -Aminu Salisu
Ni Aminu Salisu ina ganin kudi ya fi ilimi wahalar nema saboda shi ilimi kana iya samunsa a gidanka, amma kudi za ka iya tafiya wani gari nemansa ba ka same shi ba. Wani ma sai an ba shi kudin dawowa gida (in ya fita neman kudin). Da a ce mutane neman ilimi suka sa a gaba, kamar yadda suke neman kudi da kowa ya zama malami saboda saukin nemansa.