Tsakanin kamfanin WACOT da manoma a Jihar Katsina: Ina matsalar take ne?

Babu shakka danimar bana sai son barka, domin kuwa daga dukkan alamu manoma sun yi himma, Allah kuma Ya tarfa albarka a cikin daminar, domin duk inda ka duba yabanya ce koriya shar! Amma duk da haka, akwai wasu rukunin manona da suka shiga kangi a Jihar Katsina a tsakaninsu da kamfanin WACOT, mai samar […]

Tsakanin kamfanin WACOT da manoma a Jihar Katsina: Ina matsalar take ne?

Babu shakka danimar bana sai son barka, domin kuwa daga dukkan alamu manoma sun yi himma, Allah kuma Ya tarfa albarka a cikin daminar, domin duk inda ka duba yabanya ce koriya shar! Amma duk da haka, akwai wasu rukunin manona da suka shiga kangi a Jihar Katsina a tsakaninsu da kamfanin WACOT, mai samar da kayan aikin noma, kamar takin zamani, iraruwan shuka da sauransu. Domin tantance inda matsalar take, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, MALAM MUSTAPHA IBRAHIM MALUMFASHI (09039427990) ya bijiro mana da wannan tsokacin:

Da farko harkar na tafiya gwanin ban sha’awa. Manomi ya yi bayanin yawa ko fadin gonarsa da wurin da take, kamfani ya tura wakilai su gano, sannan kamfanin ya dauki bayanan gonar ya adana a na’urori, sannan ya bayar da taki buhu 8 (4 farkon damina, 4 tsakiyar damina), irin shukawa buhu 2, feshin haki gwangwani 3, hoda ta filasta jaka 2 ko 3 da kudi Naira dubu 100 ga kowacce hekta.

Jama’a na ta yabawa da wannan sauki da Allah Ya kawo ta hannun WACOT (West African Cotton Company Limited), sai kuma na ji wasu ’yan tsirarun manoma na kokawa kan nagartar takin NPK da ake ba su, wai masararsu na yin ja. Na tambayi wani jami’in WACOT kan matsalar, sai ya zargi manoman da ke kokawa da zuba takin akasin yadda kamfani ya ce a zuba, buhu 2 idan masara ta yi mako 2 da shukawa, bayan mako 2 kuma sai a nome sannan a sake zuba buhu biyun; daga nan sai a jira lokacin hudar hayi (babu maganar watsar da taki a kasa kafin hudar farko). Amma sai wasu manoman suka rika zubar da taki a kasa kafin huda, bayan mako biyu da shuka suka zuba saura buhu biyun. Wasu da gangan, wasu bisa rashin sani ko mantuwa. Ga manomin da ke da gona mai dausayi, lallai ba zai samu matsala ba, kamar yadda DEMO-FARM, watau gonakin gwaji na kamfani suka nuna. Amma ga manomin da yake noma a wuri mai tsauri, tabbas, zai iya fuskantar waccen matsala -ta yiwuwar anfanin gonarsa ya yi “ja” saboda karfin taki da karancin ruwa da ke kan gonarsa. Wasu manoman kuma sun zuba takin ne buhu 4 bayan sun yi noman farko gaba daya. Ma’ana, a takaice, kamar ba su bi shawarar da WACOT ta ba su ba.

Manoma a nasu bangaren sun zargi WACOT da kawo wa harkar tarnaki da gangan. Zargin kuma da bincike ya nuna akwai kanshin gaskiya a ciki. Da farko WACOT ta bayar da takin NPK a awannin karshe na watan biyar, watau Mayu kuma suka yi alkawarin baki (ba a rubuce ba), cewa bayan mako biyu da kammala rabon farko, za su bayar da takin UREA na hayi, watau na zubin karshe. Sai dai ba kamar yadda WACOT ya kawo tirela sama da 30 na takin NPK cikin kwanakin da ba su wuce 10 ba a farkon damina. A wannan karon, watau lokacin hudar hayi, da ya kamata a kammala a tsakiyar watan Yuli, WACOT, ya kawo kimanin tirela 10 ne a makon karshe na Yuli zuwa makon farko na Agusta (lokacin da ya kamata a ce manoma na hutu bayan kammala hayi).

Na ziyarci defo din kamfanin wanda ke Ministry of Works (M.O.W) Malumfashi a lokuta da dama, kasancewar wurin ne cibiyar bayar da kayan noman na kananan hukumomi biyar (Kafur, Malumfashi, Musawa, Kankara da Matazu), na iske manoma zaune suna jira mai kama da jiran-gawon-shanu a tsawon wadannan makonni. A takaice, WACOT, ba ta kawo takin UREA na hayi kan lokaci da kuma yawan da ya kamata ba.

Haka manoman, ganin yadda suka fadada nomansu, sun yi zargin cewa rashin ba su rancen kudin a farkon damina zai iya taimakawa a kawo matsala, kuma canza banki da aka yi a harkar, daga First Bank da Zenith zuwa U.B.A bisa (wai) jayayyar kudin ruwa, watau riba, da ba su daidaita a kai ba, shi ma zai iya taimakawa a kawo matsala. Zuwa yau 06/8/2017 da na rubuta tsokacin nan, Bankin U.B.A bai fara turo kudi ga manoman ba. Ma’ana, akwai rashin tabbataccen tsari.

Wannan rashin cikakken tsarin, shi ya janyo wani manomi ya cike fom, ya samu rijista, amma lokacin amsar  kaya sunansa ya bace. Wani kuma ya yi rijista amma ya canza shawara, ya janye daga shirin, ma’ana, ya ki amsar komai daga kamfanin, sai ga wakilin kamfanin ya kira shi, wai yana son ganin gonar da ya sanya wa kayan kamfani…

Bayan bincike, nazari ya nuna yiwuwar biye wa kalanda ko tsarin kamfani da jami’ai suka yi, maimakon la’akari da lokacin saukar ruwan sama da yadda damina ke tafiya.

Amma abin da al’umma ke tambaya shi ne: ganin kamfanin WACOT a fili ya buga sanarwa yarjejeniya da jan kunne kuma ya lika a wurare daban-daban (bayan da kowane manomi ya sanya hannu a nasa takardun) cewa ba zai dauki asara ba, ko da kuwa annoba ce daga Allah ta samu manoma, lokacin girbi (Abin Allah Ya kyauta) idan amfanin gona ya samu cikas, mene ne matakin dauka kan wadancan matsaloli da kamfanin ya haifar? Kuma a daminar badi ta 2018, da irin wannan tsarin kamfanin zai yi aiki?

Koma dai mene ne, yana da kyau gwamnati, musamman ta Jihar Katsina ta shiga tsakanin kamfanin WACOT da manoma, don kada wani ya cuci wani.