Tsakanin Likita Da dan Sanda wa ya fi amfanar da al’umma?

Aikin Likita da na dan Sanda suna da matukar muhimmanci ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin tsakaninsu wane ne aikinsa ya fi muhimmanci ga al’umma? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu dangane da wannan muhawara:   Likita yafi muhimmanci – Halima Abdullahi Rabilu Abubakar, a Gombe Halima Abdullahi: […]

Tsakanin Likita Da dan Sanda wa ya fi amfanar da al’umma?

Aikin Likita da na dan Sanda suna da matukar muhimmanci ga al’umma. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin tsakaninsu wane ne aikinsa ya fi muhimmanci ga al’umma? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu dangane da wannan muhawara:

 

Likita yafi muhimmanci – Halima Abdullahi

Rabilu Abubakar, a Gombe

Halima Abdullahi: “A nawa ra’ayin, likita ya fi dan sanda domin shi likita yana da muhimmancin da har dan sanda yana amfana da shi ta wajen kula da lafiyarsa; domin yau ko rashin lafiya mutum ya yi idan ba likita zai iya tagayyara ko da bai mutu ba. Idan yanzu mutum bai da lafiya yana fama da wata cuta da sai an yi masa tiyata, ka ga likita za a nemo ya duba shi, ya yi masa aiki idan ba haka ba kuma zai iya mutuwa ko ya yi ta zama da ciwo. Shi dan sanda ko babu shi a tsakanin al’umma babu wata matsala, domin sai fitina ta tashi sannan zai amfani jama’a kuma suna iya zama ba tashin hankali a cikinsu, ka ga kuwa ashe dan sanda ba zai yi amfani ba.”

 

dan sanda ya fi likita – Sama’ila Rogo

Abbas Ɗalibi, a Legas

Malam Sama’ila Rogo: “Bisa haƙikanin gaskiya aikin dan sanda ya fi na likita muhimmanci a rayuwar al’umma, domin sai da tsaro ne za a samu ikon zuwa wajen likita har ya yi aikinsa. Hakazalika komai rintsi komai wuya, ba za ka taɓa ji an ce ’yan sanda sun yi yajin aiki ba amma likitoci suna yawan zuwa yajin aiki. Muhimmancin aikin ’yan sanda ne ya sanya ba su yajin aiki.”

 

dan sanda ya fi likita – Alhaji Aminu

Ahmed Kabir S/kuka, a Katsina 

Alhaji Aminu Murmushin Amarya Dutsinm: “A ganina, dan sanda ya fi likita bayar da gudunmuwa a cikin al’umma saboda duk al’ummar da ba ta da jami’an tsaro, to za ta koma kamar yadda dabbobi ke rayuwa; mai karfi ya amshe wa wanda ya fi karfi, mutane za su yi rayuwa a cikin wahala da fargaba. Amma likita ko babu shi al’umma za ta iya rayuwa da maganin gargajiya.”

 

Likita ya fi amfani – Hadiza Ibrahim

Abbas dalibi, a Legas

Hajiya Hadiza Ibrahim: “Babu makawa likita ya fi dan sanda mahimmaci a rayuwar al’umma, domin likita ne ke kula da lafiyar jama’a amma za ka ga sau tari su ’yan sanda ba su kai ɗauki har sai matsala ta faru ta ƙare sannan ne za su je wajan. Shi kuwa likita kullum aikinsa ke nan kula da lafiyar jama’a.”

 

Likita ya fi dan sanda – Maryam Sani

Rabilu Abubakar, a Gombe

Maryam Sani Aliyu: “Ina mai ra’ayin cewa likita ya fi dan sanda saboda shi dan sanda ba kullum aikinsa ke tashi ba shi kuwa likita kullum yana da amfani a tsakanin al’umma saboda babu rana ko lokacin da ba a ciwo. Likita ne tushen rayuwar al’umma domin ko a unguwar da take sabuwa, al’ummar wajen sai sun fara neman asibiti kafin su nemi ofishin ’yan sanda saboda muhimmancin likita ga rayuwarsu. Ko babu dan sanda al’umma za su zauna lafiya amma idan ba likita fa ba zai yiwu ba, za a iya mutuwa. Shi kuwa dan sanda za a iya samu wani jami’n tsaro a madadinsa na ya ba da tsaro. Ka ga shi kuma likita bai da madadi.”

 

dan sanda ya fi muhimmanci – Bara’u Suleiman

Ahmed Kabir S/kuka, a Katsina 

Bara’u Suleiman Batsari: “Abin da za mu lura a nan shi ne, duk fa inda za a ce harkar tsaro ta lalace, to gaskiya akwai babbar matsala. Shi kansa likitan sai da tsaro yake zaune lafiya har ma a ce ya kula da marasa lafiya ta jiki. Amma dan sanda duka sassan biyu yake kulawa da su, wato al’umma da abin da al’ummar ta mallaka. Sai mu duba mu gani likitoci suna shiga yajin aiki amma kuma al’umma na ci gaba da harkokinsu na yau da kullum babu wata damuwa amma inda a ce dan sanda zai yi yajin aiki koda na awa daya ne, yaya ake ganin rayuwar za ta kasance?”