Tsakanin Majalisar Tarayya da Al’umma: Wa ya kamata ya amince da taron kasa?
An dauki lokaci ana cece-kuce game da taron kasa da ake kokarin shiryawa. Wasu na ganin cewa majalisun kasa ne ya kamata su amince da taron, a yayin da wasu kuma ke cewa al’ummar kasa ya kamata su kada kuri’ar amincewa da yinsa. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu wa ya kamata ya amince […]
An dauki lokaci ana cece-kuce game da taron kasa da ake kokarin shiryawa. Wasu na ganin cewa majalisun kasa ne ya kamata su amince da taron, a yayin da wasu kuma ke cewa al’ummar kasa ya kamata su kada kuri’ar amincewa da yinsa. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu wa ya kamata ya amince da taron? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin al’umma kan batun, kamar haka:
’Yan majalisa ya kamata su amince – Harisu Hamisu
Harisu Hamisu Dutsin-ma: “Wadanda ya kamata su tsara taron kasa su ne ’yan majalisar kasa, wadanda dama ke da masaniya a kan al’amuran kasa wadnda suka shafi yankunansu da kuma wasu yankunan daban. Dama jama’a sun zabe su ne don su wakilce su a al’amuran kasa.”