Tsakanin Majalisar Tarayya da Al’umma: Wa ya kamata ya amince da taron kasa? 1
An dauki lokaci ana cece-kuce game da taron kasa da ake kokarin shiryawa. Wasu na ganin cewa majalisun kasa ne ya kamata su amince da taron, a yayin da wasu kuma ke cewa al’ummar kasa ya kamata su kada kuri’ar amincewa da yinsa. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu wa ya kamata ya amince […]
An dauki lokaci ana cece-kuce game da taron kasa da ake kokarin shiryawa. Wasu na ganin cewa majalisun kasa ne ya kamata su amince da taron, a yayin da wasu kuma ke cewa al’ummar kasa ya kamata su kada kuri’ar amincewa da yinsa. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu wa ya kamata ya amince da taron? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin al’umma kan batun, kamar haka:
Hakkin ’yan majalisa ne – Malama Hajara Musa
Malama Hajara Musa Adamu: “A ra’ayina, bai dace a ji ra’ayin jamaa ba, domin akwai ’yan majalisar kasa da aka zaba daga kowane laugun kasar nan domin su kare hakkin mutane. Don haka kuwa a bar su su yi duk abin da ya dace, domin kuwa idan wadannan sun gama zagayen su to dole sai sun sa albarka a kan abin. In kuwa haka ne, to wahalar da jama’a za a yi kuma a bata kudi domin jin ra’ayin jama’a yaudara ne.”