Tsakanin Majalisar Tarayya da Al’umma: Wa ya kamata ya amince da taron kasa? 2
An dauki lokaci ana cece-kuce game da taron kasa da ake kokarin shiryawa. Wasu na ganin cewa majalisun kasa ne ya kamata su amince da taron, a yayin da wasu kuma ke cewa al’ummar kasa ya kamata su kada kuri’ar amincewa da yinsa. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu wa ya kamata ya amince […]
An dauki lokaci ana cece-kuce game da taron kasa da ake kokarin shiryawa. Wasu na ganin cewa majalisun kasa ne ya kamata su amince da taron, a yayin da wasu kuma ke cewa al’ummar kasa ya kamata su kada kuri’ar amincewa da yinsa. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu wa ya kamata ya amince da taron? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin al’umma kan batun, kamar haka:
Majalisa ta dace da amincewa – Muhammad Sani
Muhammad Sani Ibrahim: “’Yan majalisa ne ya kamata su tsara, wadanda dama jama’ar ne suka zabe su su wakilce su a al’amuran kasa amma a yadda abun yake a yanzu, wasu mutane ne da Shugaban kasa ya zabe su da niyyar su tsara masa abin da yake so, ba abin da al’ummar kasa ke so ba.”