Tsakanin Majalisar Tarayya da Al’umma: Wa ya kamata ya amince da taron kasa? 3
An dauki lokaci ana cece-kuce game da taron kasa da ake kokarin shiryawa. Wasu na ganin cewa majalisun kasa ne ya kamata su amince da taron, a yayin da wasu kuma ke cewa al’ummar kasa ya kamata su kada kuri’ar amincewa da yinsa. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu wa ya kamata ya amince […]
An dauki lokaci ana cece-kuce game da taron kasa da ake kokarin shiryawa. Wasu na ganin cewa majalisun kasa ne ya kamata su amince da taron, a yayin da wasu kuma ke cewa al’ummar kasa ya kamata su kada kuri’ar amincewa da yinsa. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu wa ya kamata ya amince da taron? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin al’umma kan batun, kamar haka:
Hakkin jama’ar kasa ne – Iro Makanike
Alhaji Iro Makanike: “Sam-sam ba wani amfani, in kuwa har ana so a yi taron; to sai a rusa majalisun kasa da shi kansa wanda ya kira taron, wato mai zauran baki daya kuma a kafa Majalisar kasa mai cikakken iko, domin jin ra’ayin jama’a. In kuwa ba haka ba, to a bari ’yan majalisar kasa su yi aikin su kawai; kada a yaudari mutane.”