Tsakanin Majalisar Tarayya da Al’umma: Wa ya kamata ya amince da taron kasa? 4
An dauki lokaci ana cece-kuce game da taron kasa da ake kokarin shiryawa. Wasu na ganin cewa majalisun kasa ne ya kamata su amince da taron, a yayin da wasu kuma ke cewa al’ummar kasa ya kamata su kada kuri’ar amincewa da yinsa. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu wa ya kamata ya […]
An dauki lokaci ana cece-kuce game da taron kasa da ake kokarin shiryawa. Wasu na ganin cewa majalisun kasa ne ya kamata su amince da taron, a yayin da wasu kuma ke cewa al’ummar kasa ya kamata su kada kuri’ar amincewa da yinsa. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu wa ya kamata ya amince da taron? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin al’umma kan batun, kamar haka:
Majalisa take da hurumin amincewa
– Ado Shu’aibu
Alhaji Ado Shu’aibu dansudu: “Majalisa ce ya kamata a ce ta amince a yi taron amma da zarar sun amince an yi taron to sai su sauka daga kan mukamansu, domin sun amince da wani abu da ba ya cikin doka kuma ba ya kan tsari. Taron bai dace a ce an yi shi ba.”