Tsakanin Majalisar Tarayya da Al’umma: Wa ya kamata ya amince da taron kasa? 5
An dauki lokaci ana cece-kuce game da taron kasa da ake kokarin shiryawa. Wasu na ganin cewa majalisun kasa ne ya kamata su amince da taron, a yayin da wasu kuma ke cewa al’ummar kasa ya kamata su kada kuri’ar amincewa da yinsa. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu wa ya kamata ya amince […]
An dauki lokaci ana cece-kuce game da taron kasa da ake kokarin shiryawa. Wasu na ganin cewa majalisun kasa ne ya kamata su amince da taron, a yayin da wasu kuma ke cewa al’ummar kasa ya kamata su kada kuri’ar amincewa da yinsa. Abin tambaya a nan shi ne, tsakaninsu wa ya kamata ya amince da taron? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin al’umma kan batun, kamar haka:
Majalisa ce ya kamata ta amince da taron – Nasiru Gulma
Alhaji Nasiru Gulma: “Da farko dai ni ban yarda cewa taron nan za a yi shi saboda Allah ba. Ni a wurina, ina ganin ya kamata a yi wa kowane bangare adalci amma majalisa ce ya kamata ta tsara yadda ya kamata a yi taron kuma ita ya kamata a ce ta amince a yi shi saboda su ne suke yin dokoki.”